- Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana dalilan da suka janyo karancin kudin Naira a kasar
- Wannan dai na zuwa ne biyo bayan korafe-korafen da wasu kwastomomin bankuna suka yi kan karancin kudin da ake samu na Naira a Bankuna
- Tuni CBN ya ce babu karancin kudin Naira sannan akwai wadatattun kudaden a tattalin arzikin Najeriya
Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dalilan da suka janyo karancin kudin Naira a kasar.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan korafe-korafen da wasu kwastomomin bankuna suka yi kan karancin kudin da ake samu na Naira a Bankuna da na’urar cirar Kudi ta ATM da wuraren Masu PoS, da kasuwannin canjin kudaden waje BDCs.
KARANTA WANNAN: Dalilin Da Yasa Ba Ni da Group na WhatsApp Tare da Messi, Neymar – Suarez
A cikin wata sanarwa da Sashen Sadarwa na Babban Bankin na CBN ya fitar, babban bankin ya ce ana ganin karancin kudin ne ya biyo bayan wasu makudan kudade da DMBs suka yi na cire kudade daga rassa daban-daban na CBN.
Ya bayyana cewa firgici cirar kudade da abokan cinikin banki ke yi shi ma wani bangare ne da ya haddasa karancin.
Babban bankin na CBN ya ce babu karancin kudin Naira, yana mai cewa akwai wadatattun kudaden a tattalin arzikin kasar.
“An jawo hankalin CBN akan rahotannin da ake zargin ana fama da karancin kudi a bankuna, ATMs, PoS da BDC a wasu manyan biranen kasar nan.
“Binciken da muka yi ya nuna cewa ana ganin karancin kudi a wasu wuraren ya samo asali ne saboda yawan cire kudi daga rassan CBN da DMBs suka yi da kuma firgita da kwastomomin da ke cirewa daga na’urar ATM.
“Yayin da muka lura da damuwar ‘yan Najeriya kan yadda ake samun tsabar kudi domin hada-hadar kudi, muna so mu tabbatar wa jama’a cewa akwai isassun takardun kudi na ayyukan tattalin arziki a kasar nan.
“Sassan bankin na CBN a fadin kasar nan kuma suna aiki don tabbatar da cewa an samu raguwar kudaden a jihohinsu na aiki,” inji shi.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, CBN ya gabatar da sabbin takardun kudi na N200, N500 da N1,000 a watan Oktobar shekarar 2022 kuma an sanya wasu wa’adin da aka sanya na daina Amfani da wadannan takardun kudi a matsayin doka.
A wani labarin kuma, Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Taya TY Danjuma Murnar Cika Shekaru 86 a Duniya
Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya taya TY Danjuma murnar cika shekaru 86 a Duniya
TY Danjuma ya kasance “A kowanne lokaci yana nuna jarumtakar soja da ƙarfin hali. Sannan ya yi wa sojoji hidima da alfahari”
Bayan ya yi ritaya, TY Danjuma ya ci gaba da yi wa Najeriya hidima a matsayin ministan tsaro a gwamnatin Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya buga waya domin taya murnar cika shekaru 86 na Janar Theophilus Yakubu Danjuma mai ritaya, musamman domin nuna godiya da kuma nuna jin dadinsa kan aikin soja da aka kawata da ya yi a kasar.
“T.Y. Danjuma kamar yadda babban hafsan sojin kasa ya gina rundunar sojojin da ke shirin aiwatar da ayyukan yaki ba dare ba rana, a gida da waje,” Buhari ya nakalto cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi.