NDLEA ta cika hannu da matasan da suka shirya gasar shan miyagun ƙwayoyi a Katsina
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, sun tarwatsa wata gasar shan miyagun kwayoyi da aka shirya yi ta murnar kafin daurin aure a unguwar Shola Quarters da ke cikin birnin Katsina tare da cafke wasu matasa 25 da aka kama a bikin sha ƙwaya.
Dangane da bayanan sirri, jami’an sun kai farmaki kan wadanda ake zargin ne a yayin da suke kan shagaltuwa da shan miyagun kwayoyi da suka zuba kwayoyi da dama a cikin bokitin roba da ruwa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dalilin Da Yasa Ba Ni da Group na WhatsApp Tare da Messi, Neymar – Suarez
Duk da cewa angon, Musa Gwandi, wanda ya shirya bikin shan miyagun kwayoyi tare da wasu abokansa, ba sa wajen taron a lokacin da aka kama mutane 25, amma an kama shi a ranar Lahadi 3 ga watan Disamba, sakamakon farautar sa da aka yi.
A wani labarin kuma:Ta’addanci: ECOWAS za ta kafa wasu dakaru na musamman
Shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, sun kafa wata hanya da za ta sake duba kokarin da ake yi na samar da rundunar da za ta yaki ayyukan ta’addanci, musamman a yankunan da kungiyoyin ‘yan ta’adda suka mamaye.
Hakan ya biyo bayan wani kuduri ne a karshen taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS karo na 64, ranar Lahadi a Abuja.