- Babban bankin Najeriya, CBN, ya dakatar da biyan kudaden da ake kashewa a kan wasu makudan kudade
- Daukar wannan matakin na zuwa Ne Yayin da Karancin Kudin Naira Ke Kara Kamari a Najeriya
- Duk cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke kula da su ya kamata su karbi duk kudaden ajiye daga hannun jama’a ba tare da an karbi kudade a wajen su ba
Babban bankin Najeriya, CBN, ya dakatar da biyan kudaden da ake kashewa a kan wasu makudan kudade, Daily Post ta rahoto.
Mukaddashin Daraktan Sa ido na CBN, Dr Adetona Adedeji, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN: ‘Ba Zan Gamsu Ba Har Sai An Kawo Karshen Rashin Tsaro a Najeriya’ – Tinubu
Sabon ci gaban a ƙarƙashin “Jagorar cajin Bankuna, Sauran Cibiyoyin Kuɗi, da Cibiyoyin Kuɗi da ba na Bankunan ba” da aka bayar a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 2019, tare da lamba (FPR/DIR/GEN/CIR/07/042), yana shafar ajiyar kudi na sama da Naira dubu N500,000 na asusun mutum daya da Naira Dudu N3,000,000 na asusun kamfani.
Babban bankin ya ce dakatarwar za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar 30 ga watan Afrilu, 2024.
Babban bankin na CBN ya kuma bayyana cewa a asusun kamfanoni, bankunan ajiya za su rika karbar kudaden sarrafawa kashi biyar bisa dari na kudaden da za a cire da kuma kashi uku bisa dari na kudaden da aka ajiye a sama da Naira dubu N3,000,000.
“Saboda haka, duk cibiyoyin hada-hadar kudi da CBN ke kula da su ya kamata su karbi duk kudaden ajiye daga hannun jama’a ba tare da an karbi kudade a wajen su ba,” in ji CBN.
A wani labarin kuma, Nasarawa: Daliban Jami’ar FULAfiya Takwas da Aka Sace Sun Shaki Iskar ‘Yanci
Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULafia) dake Jihar Nasarawa sun sake samun ‘yanci daga hannun wadanda suka sace su
Tuni dukkan daliban da aka sace suka sake haduwa da iyalansu
Tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da jami’an tsaro an kara tsaurara matakan tsaro a jami’ar da kewaye domin dakile afkuwar lamarin nan gaba
Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULafia) dake Jihar Nasarawa sun sake samun ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a daren ranar Laraba 6 ga watan Disamba ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu dalibai a unguwar Gandu da ke kusa da makarantar.