- Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULafia) dake Jihar Nasarawa sun sake samun ‘yanci daga hannun wadanda suka sace su
- Tuni dukkan daliban da aka sace suka sake haduwa da iyalansu
- Tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da jami’an tsaro an kara tsaurara matakan tsaro a jami’ar da kewaye domin dakile afkuwar lamarin nan gaba
Daliban Jami’ar Tarayya ta Lafia (FULafia) dake Jihar Nasarawa sun sake samun ‘yanci daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa a daren ranar Laraba 6 ga watan Disamba ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu dalibai a unguwar Gandu da ke kusa da makarantar.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Gwamnan Ribas Fubara Ya Kira Taron Gaggawa Bayan ‘Yan Majalisa 27 Sun Koma APC
Da yake tabbatar da sakin ga Tribune Online ta wayar tarho a ranar Litinin a Lafiya, Abubakar Ibrahim, shugaban yada labarai da hulda da jama’a na Jami’ar, ya ce an sako 8 daga cikin daliban da misalin karfe 8:00 na daren ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba.
Malam Ibrahim ya kara da cewa dukkan daliban sun sake haduwa da iyalansu.
Hakazalika, tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar da jami’an tsaro, kakakin ya kuma bayyana cewa, hukumar ta kara tsaurara matakan tsaro a jami’ar da kewaye domin dakile afkuwar lamarin nan gaba.
Har ila yau, Malam Hassan Kassimu, shugaban al’ummar Gandu da aka yi garkuwa da daliban, ya ce an kai su cibiyar kula da lafiya ta jami’ar domin duba lafiyarsu.
A wani labarin kuma, Dalilan da Suka Sanya Aka Samu Karancin Naira a Najeriya — CBN
Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana dalilan da suka janyo karancin kudin Naira a kasar
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan korafe-korafen da wasu kwastomomin bankuna suka yi kan karancin kudin da ake samu na Naira a Bankuna
Tuni CBN ya ce babu karancin kudin Naira sannan akwai wadatattun kudaden a tattalin arzikin Najeriya
Babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana dalilan da suka janyo karancin kudin Naira a kasar.
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan korafe-korafen da wasu kwastomomin bankuna suka yi kan karancin kudin da ake samu na Naira a Bankuna da na’urar cirar Kudi ta ATM da wuraren Masu PoS, da kasuwannin canjin kudaden waje BDCs.