- Mai shari’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya ya sanya ranar yanke hukunci kan aiwatar da wasu muhimman kararrakin da tsohon gwamnan CBN Emefiele ya shigar
- Alkalin kotun ya tsayar da ranar ne bayan ya saurari bahasi daga bangarorin da ke karar
- Tsohon Gwamnan na CBN ya shigar da Kara kan tauye masa Hakkokin Sa na rayuwa
Mai shari’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya a ranar Litinin ya sanya ranar 8 ga watan Janairu domin yanke hukunci kan aiwatar da wasu muhimman kararrakin da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefiele ya shigar.
Alkalin ya tsayar da ranar ne bayan ya saurari bahasi daga bangarorin da ke karar.
KARANTA WANNAN: Kano: EFCC ta Gurfanar da Wasu Ma’aurata Kan Zargin Zambar N410m
Haka kuma ya kebe hukuncin a cikin karar farko da duk wadanda aka shigar da kara su hudu suka shigar, mai lamba FCT/HC/CV/040/2023.
Emefiele da ya shiga tsakani ya kai Gwamnatin Tarayya da Babban Lauyan Tarayya, AGF, Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin kasa Tu’annati (EFCC) da kuma ita kanta Hukumar a gaban Kotu, domin ta aiwatar da muhimman hakkokinsa na rayuwa, ‘yancin kai, sauraron shari’ar gaskiya da ‘yancin motsi.
Emefiele ya nemi kotu ta ba da sanarwar cewa ci gaba da tsare shi da hukumar ta yi na wadanda ake kara na daya da na biyu tun daga ranar 10 ga watan Yunin 2023, sannan aka mika shi hannun wadanda ake kara na uku da na hudu a ranar 26 ga watan Oktoba, 2023, ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba haramun ne.
Ya ce, bijirewar da wadanda ake kara suka yi na wasu ingantattun umarnin kotu na a sake shi, tamkar cin zarafi ne na hakokinsa na rayuwa da kuma ‘yancin kai kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da kuma kundin tsarin mulkin dan Adam na Afirka suka tabbatar da Hakkoki.
Don haka Emefiele, da sauransu, ya nemi umarnin hana wadanda ake karan daga ci gaba da kama shi da/ko kuma su ci gaba da tsare shi a lokacin da kotu ta sake shi ba tare da tuhumarsa da aikata laifi ba.
Ya kuma nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 1 saboda tauye masa hakkinsa.
A wani labarin kuma, Majalisar Dattijai Ta Fusata Kan Rashin Kammala Ayyukan Hanyoyin da ‘Yan Kwangila Ke Yi
Majalisar dattijai ta nuna rashin jin dadi kan rashin kammala ayyukan hanyoyin da ‘yan kwangila ke yi a fadin kasar nan
Da yawan hanyoyi sun shafe shekaru sama da 20 ana gina su mun lura da samar da kasafin kudi amma ba a kammala ba kuma kusan kullum ana asarar rayuka da dama
Bisa fusatar data yi majalisar dattawa tace za ta daina komai don ganin ba a barnata kudaden gwamnati da kudaden masu biyan haraji ba
Majalisar dattijai a ranar Litinin ta nuna rashin jin dadi kan rashin kammala ayyukan hanyoyin da ‘yan kwangila ke yi a fadin kasar nan.
Shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa Sanata Mpigi Barinada ne ya bayyana haka a lokacin da ministan ayyuka David Umahi ya bayyana a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar kan ayyukan kare kasafin kudin shekarar 2024.