- Jam’iyyar LP, ta yi kira ga kakakin majalisar dokokin Ribas ya bayyana kujerun ‘yan majalisa 27 da suka koma APC a matsayin wadanda ba kowa ba
- LP ta yi kiran da a sake sabon zabe domin cike guraben kujerun Wadanda Suka sauya shekar
- Jam’iyyar LP ta bayyana sauya shekar a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa
Jam’iyyar Labour Party, LP, ta yi kira ga kakakin majalisar dokokin jihar Ribas da ya bayyana kujerun ‘yan majalisa 27 da suka koma jam’iyyar APC a matsayin wadanda ba kowa ba.
Ita ma shugabar jam’iyyar LP ta Jihar Ribas, Hilda Dokubo, ta yi kira da a sake sabon zabe domin cike guraban kujeru.
KARANTA WANNAN: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunci Kan Muhimman Hakkokin Emefiele
A wata sanarwa da ta sanyawa hannu, Dokubo ta bayyana sauya shekar a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.
A cewar Dokubo: “Taron ya fito karara kan makomar ‘yan majalisar da suka ci amanar jam’iyyar da ta dauki nauyinsu.
“Saboda haka, Labour ta bukaci shugaban majalisar ya bayyana kujeru 27 a matsayin ba kowa a kansu nan take.
“Yakamata ‘yan siyasa su sani cewa ba za su iya kara daukar masu zabe da jam’iyyun da suka dauki nauyinsu ba.
“Sabon zabukan da za a yi a jihar Ribas zai baiwa jama’a damar zaben wakilansu na gaskiya.”
A wani labarin kuma, Majalisar Dattijai Ta Fusata Kan Rashin Kammala Ayyukan Hanyoyin da ‘Yan Kwangila Ke Yi
Majalisar dattijai ta nuna rashin jin dadi kan rashin kammala ayyukan hanyoyin da ‘yan kwangila ke yi a fadin kasar nan
Da yawan hanyoyi sun shafe shekaru sama da 20 ana gina su mun lura da samar da kasafin kudi amma ba a kammala ba kuma kusan kullum ana asarar rayuka da dama
Bisa fusatar data yi majalisar dattawa tace za ta daina komai don ganin ba a barnata kudaden gwamnati da kudaden masu biyan haraji ba
Majalisar dattijai a ranar Litinin ta nuna rashin jin dadi kan rashin kammala ayyukan hanyoyin da ‘yan kwangila ke yi a fadin kasar nan.
Shugaban kwamitin ayyuka na majalisar dattawa Sanata Mpigi Barinada ne ya bayyana haka a lokacin da ministan ayyuka David Umahi ya bayyana a gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin kasar kan ayyukan kare kasafin kudin shekarar 2024.