- Yayin da ake ci gaba da zafafa rikicin jihar Ribas, yanzu haka kwamishinoni hudu sun yi murabus daga gwamnatin gwamna Siminalayi Fubara
- Wannan na zuwa ne bayan da babban mai shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a ya yi murabus daga majalisar ministocin Fubara
- Rikicin da ya barke a jihar ya dauki sabon salo a lokacin da ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar Nyesome Wike Suka sauya sheka
Yayin da ake ci gaba da zafafa rikicin jihar Ribas, yanzu haka kwamishinoni hudu sun yi murabus daga Majalisar zartarwar gwamna Siminalayi Fubara.
Kwamishinan walwala na jihar, Inime Chinwenwo-Aguma, da kwamishinan ayyuka, George-Kelly Alabo, na daga cikin wadanda suka yi murabus cikin sa’o’i 24.
KARANTA WANNAN: Jami’an NSCDC Sunyi Ram da Wasu Barayin Mai Guda Biyar
Chinwenwo-Aguma ya ba da misali da “aiki na kashin kansa da sauran alƙawura,” yayin da Alabo ya ce ya yi murabus ne bisa “lamirinsa” kamar yadda aka gani a cikin sanarwar manema labarai.
Wannan na zuwa ne bayan da babban mai shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a, Farfesa Zacchaeus Adangor, SAN, da kwamishinan ayyuka na musamman, Emeka Woke, suka yi murabus daga majalisar ministocin Fubara.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa rikicin da ya barke a jihar ya dauki sabon salo a lokacin da ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga tsohon gwamnan jihar Nyesome Wike suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Don haka ‘yan majalisar da ke biyayya ga gwamnan jihar sun bayyana kujerunsu a matsayin babu kowa, yayin da suke kira ga hukumar zabe mai zaman kanta da ta gudanar da sabon zabe domin maye gurbinsu.
Har ila yau, a ranar Larabar da ta gabata gwamnatin jihar ta rusa harabar majalisar, inda ta ce ba ta da aminci ga harkokin majalisar.
A wani labarin kuma, ‘Ka Daina Nuna Kanka a Matsayin Ministan Man Fetur’ – Falana Ga Shugaba Tinub
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana ya shaidawa shugaban kasa Bola Tinubu cewa ya daina bayyana kansa a matsayin ministan albarkatun man fetur
Lauyan ya gargadi Tinubu da kada ya yi koyi da Wasu tsaffin shugabannin kasar Najeriya
A cewar Lauyan rawar da Tinubu ke takawa a matsayin Ministan Albarkatun Man Fetur ya sa kasar nan ke da wahala wajen rike NNPC
Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana ya shaidawa shugaban kasa Bola Tinubu cewa ya daina bayyana kansa a matsayin ministan albarkatun man fetur.
Falana ya bayar da hujjar cewa matsayin shugaban kasa a matsayin ministan man fetur ya sabawa sashe na 147 na kundin tsarin mulki, inda ya gargadi Tinubu da kada ya yi koyi da tsaffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari.