- Gwamnan Oyo, Seyi Makinde a hukumance ya mika sandar mulki ga sabon basaraken Aseyin na Iseyin, Oba Sefiu Oyebola, Adeyeri III, Ajirotutu I
- Tun da farko wani lauya ya Gargadi Gwamna Makinde da kada ya ci gaba da gabatar da sandar mulki ga sabon basaraken
- Gwamnan wanda ya gabatar da sandar mulki ga sabon basaraken ya bayyana cewa bunkasa garin na Iseyin shi ne babban abin da ke damun sa
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, a ranar Alhamis, a hukumance ya mika sandar mulki ga sabon Aseyin na Iseyin, Oba Sefiu Oyebola, Adeyeri III, Ajirotutu I.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa tun da farko wani lauya Abideen Adeniran ya shawarci Makinde da kada ya ci gaba da gabatar da sandar mulki ga sabon Aseyin saboda har yanzu shari’ar da ke kalubalantar zaben sa na kan gaban wata babbar kotun jihar Oyo da ke zaune a Iseyin.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Cikin Sa’oi 24 Kwamishinoni Hudu Sun Yi Murabus Daga Gwamnatin Fubara
Adeniran, wanda ya kuma bayyana cewa matakin ya zama wajibi domin tabbatar da adalci, zaman lafiya da kuma shugabanci na gari, ya kuma kara da cewa kamata ya yi gwamnati a karkashin jagorancin Makinde ta lura da batun dakatar da kara mai lamba HOI/04/2023 a gaban Kotun dake zaune a Iseyin, a kan fafatawa kan Kujerar ta tsohon garin.
Sai dai Makinde, wanda ya gabatar da sandar mulki ga sabon Aseyin a filin wasa na Iseyin, ya bayyana cewa bunkasa garin na Iseyin shi ne babban abin da ke damun sa, inda ya kara da cewa garin na da matukar girma da ci gaba.
Ya ce, “Iseyin gari ne mai dimbin fa’ida, kuma na kuduri aniyar hada hannu da jama’ar Iseyin domin amfani da wannan damar domin amfanin kowa.
Sannan Gwamnan ya ce “Ilimi da karfafa matasa su ne ginshikin makoma mai albarka ga Iseyin. Idan aka samu jarin da ya dace a wadannan fannoni, za mu iya tabbatar da cewa matasanmu sun samu kwarewa da ilimin da suke bukata domin samun nasara.”
Gwamnan ya kuma kara jaddada cewa tuni gwamnatin sa ta fara aiwatar da wasu tsare-tsare na inganta ilimi da inganta rayuwar matasa a garin, inda ya yi alkawarin yin aiki don jawo jarin Iseyin, tare da mai da hankali kan harkar noma.
A martanin da ya mayar bayan gabatar da jawabin, basaraken Oba Oyebola, wanda ya nuna godiyarsa ga gwamnan, ya ce wannan wani muhimmin lokaci ne a gare shi da kuma al’ummar Iseyin.
Ya ce, “Ina matukar godiya ga Gwamna Makinde bisa goyon bayan da ya ba ni, da kuma irin kwarin gwiwar da ya nuna mini ta hanyar gabatar mun da sandar mulki. Na jajirce wajen hada kai da gwamna domin inganta cigaban garin mu.
“A matsayina na Aseyin na Iseyin, zan tabbatar da cewa mutanen Iseyin suna alfahari da al’adun gargajiya da kuma ci gaba da kiyaye dabi’u da al’adun da suka sa garinmu ya zama na musamman.”
Don haka Oba Oyebola, ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin ganin yadda al’ummar garin suke bukata, da samar da zaman lafiya da hadin kai, da bunkasa tattalin arziki.
A wani labarin kuma, Jami’an NSCDC Sunyi Ram da Wasu Barayin Mai Guda Biyar
Jami’an rundunar farin kaya (CG’s SIS) na hukumar tsaron NSCDC sun cafke wasu mutane biyar da ake zargi da satar mai
Rundunar ta kama wadanda ake zargin ne a yayin da suke isar da wasu makudan kayan da ake zargin taceccen Mai ne ba bisa ka’ida ba
Simamen ya biyo bayan samun bayanan Sirri kan Masu aikata laifukan
Jami’an rundunar farin kaya (CG’s SIS) na hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) sun cafke wasu mutane biyar da ake zargi da satar mai a jihar Imo.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Babawale Afolabi shine wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar din da ta gabata, inda ya ce rundunar ta kama wadanda ake zargin ne a yayin da suke isar da wasu makudan kayan da ake zargin taceccen Mai ne ba bisa ka’ida ba, da kuma gurbataccen AGO a yankin Obah Agwa mai cin gashin kanta da ke karamar hukumar Oguta Ohaji ta jihar Imo.