- Masanin ‘yan wasa Fabrizio Romano ya bayyana cewa Chelsea ba ta Wata tattaunawa da zakarun Seria A Napoli akan Victor Osimhen
- Dan wasan yana cikin jerin ‘yan wasan da Chelsea ke nema
- Dan wasan ya ci kwallaye bakwai a wasanni 12 da ya buga wa Partenopei a kakar wasa ta bana
Masanin ‘yan wasa Fabrizio Romano ya bayyana cewa Chelsea ba ta wata tattaunawa da zakarun Seria A Napoli akan Victor Osimhen.
Ana sa ran Osimhen zai rattaba hannu kan sabon kwantaragi da Napoli wanda zai hada da batun sakin kusan Yuro miliyan 130.
KARANTA WANNAN: Kirsimeti: FRSC Ta Fara Sintiri Na Sa’o’i 24 a Fadin Najeriya
Ana kyautata zaton har yanzu Chelsea na zawarcin dan wasan na Najeriya.
Blues na neman siyan gogaggen mutumin da ake nema kuma suna da dan wasan mai shekaru 24 akan komar su.
Romano ya rubuta a cikin jaridar Daily Briefing cewa, “Osimhen yana cikin jerin ‘yan wasan da Chelsea ke nema amma har yanzu babu wata shawara da aka yanke ko wani ci gaba da tattaunawa da dan wasan gaba ko wani dan wasa”.
Osimhen ya ci kwallaye bakwai a wasanni 12 da ya buga wa Partenopei a kakar wasa ta bana.
A wani labarin kuma,Da Dumi-Dumi: Rikicin Rivers, Wike da Gwamna Fubara sun rattaba hannu kan Wata Yarjejeniya
Gwamnan Ribas Sim Fubara da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike hava, sun amince da kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar
Hakan na zuwa ne bayan da Shugaban Kasa Tinubu ya gada Gwamnan da Wanda ya gada
Kafin yanzu Rikicin Siyasar Rivers ya dauki Sabon Salo Daga bangarorin biyu
Gwamna Sim Fubara na jihar Ribas da kuma wanda ya gada, Nyesom Wike hava, sun amince da kawo karshen rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar.