- Wani mutum a jihar Adamawa mai suna Linus Dimas ya kashe magatakardar kotu da aka aika masa
- Tunda farko wanda ake zargin ya ki amincewa da sammacin kotun da magatakardar kotun ya kai masa
- Tuni Jami’an ‘yan sanda Suka dukufa Domin Gudanar da cikakken Bincike Kan lamarin
Wani mutum a jihar Adamawa mai suna Linus Dimas ya kashe magatakardar kotu da aka aika masa domin ya gayyace shi zuwa kotu.
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai a yammacin ranar Talata, inda ta ce jami’anta sun kama wanda ake zargin a ranar Litinin, 18 ga watan Disamba, a lokacin da ake zargin ya kashe magatakardar Kotu da ya je ya Kai masa takardar sammacin kotu.
KARANTA WANNAN: Nottingham Forest ta kori kocinta Steeve Cooper
Sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda Suleiman Nguroje, ta ce Linus Dimas mai shekaru 43, mazaunin Kugama Wuro Jibir ne a karamar hukumar Mayo Belwa.
A cewar sanarwar: “Wanda ake zargin, a ranar 18 ga watan Disamba, 2023, ya ki amincewa da sammacin kotu da Yauba Usman, magatakardar kotun yankin Nasarawo Jereng ya Kai masa inda wadanda Ake Zargin suka kai masa hari tare da daba masa wuka da dama, wanda hakan ya yi masa rauni sosai.”
Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa, nan take aka garzaya da magatakardar kotun zuwa asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Sanarwar ta kara da cewa “Kwamishanan ‘yan sandan ya bada umarnin a binciki lamarin cikin hikima.”
A wani labarin kuma, Gwamnan Osun Adeleke Ya Dage Dokar Hana Fita Daya Sanya a Jihar
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin a dage dokar hana fita da aka Sanya a Wasu kananan hukumomin Biyu dake Jihar
Kafin da ge Dokar an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kananan hukumomin biyu biyo bayan kazamin fadan da ya haifar da rashin jituwa a kan iyaka
Kwamishinan ya ce an dage dokar hana fita ne bayan gwamnati ta lura cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin a dage dokar hana fita da aka Sanya a kananan hukumomin Irepodun da Orolu daga ranar Laraba.
Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Kolapo Alimi, wanda ya fitar a Osogbo ranar Talata.