- Kungiyar Kwallon kafa ta Nottingham Forest ta sallami kocinta Steve Cooper
- An kori kocin bayan rashin nasara daya samu a wasanni 13 na gasar Firimiya
- Dan wasan mai shekaru 44 yana shan suka a duk lokacin da ya yi rashin nasara
Kungiyar Kwallon kafa ta Nottingham Forest ta sallami kocinta Steve Cooper ranar Talata a daidai lokacin da rahotanni ke cewa masu gwagwarmayar gasar Premier na shirin daukar Nuno Espirito Santo.
An kori Cooper bayan rashin nasara daya samu a wasanni 13 na gasar Firimiya wanda ya bar Forest a matsayi daya a saman matakin faduwa.
KARANTA WANNAN: Musaya: Chelsea Ba ta Wata Tattaunawa da Napoli kan Dan Wasa Osimhen – Romano
Dan wasan mai shekaru 44 ya sha suka a duk lokacin da ya yi rashin nasara daya kacal a wasanni 13, ciki har da shan kashi biyar a wasanni shida da suka yi.
An bayar da rahoton cewa, Forest ya tattauna da tsohon kocin Tottenham da Wolves Nuno game da komawa gasar Premier a safiyar ranar Talata.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce “A yau an kori Steve Cooper daga mukaminsa na kocin Nottingham Forest, bayan shafe sama da shekaru biyu yana jan ragamar kungiyar.”
“Kungiyar za ta kara ba da sanarwar nadin sabon koci a kan lokaci.”
A wani labarin kuma, Gwamnan Osun Adeleke Ya Dage Dokar Hana Fita Daya Sanya a Jihar
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin a dage dokar hana fita da aka Sanya a Wasu kananan hukumomin Biyu dake Jihar
Kafin da ge Dokar an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a kananan hukumomin biyu biyo bayan kazamin fadan da ya haifar da rashin jituwa a kan iyaka
Kwamishinan ya ce an dage dokar hana fita ne bayan gwamnati ta lura cewa an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin a dage dokar hana fita da aka Sanya a kananan hukumomin Irepodun da Orolu daga ranar Laraba.
Umurnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mista Kolapo Alimi, wanda ya fitar a Osogbo ranar Talata.