- Yanzu haka dai an rantsar da tsohon Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Simon Lalong a matsayin Sanata
- Kafin rantsar da shi tsohon ministan ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasa Bola Tinubu
- Wannan dai na zuwa ne bayan kammala shari’ar da kotun daukaka kara ta bayyana shi a matsayin zababben dan majalisar dattawa
An rantsar da tsohon Ministan Kwadago da Samar da Ayyukan yi, Simon Lalong a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu.
Lalong, wanda tsohon gwamnan jihar Filato ne an rantsar da shi a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: Ministan Kwadago Ya Yi Murabus a Hukumance Don Darewa Kujerar Sanata
Tsohon ministan ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Talata.
An tabbatar da murabus din Lalong a cikin wata sanarwa da mai ba wa minista mai barin gado shawara kan harkokin yada labarai, Dr Makut Simon Maham ya sanya wa hannu.
Ta bayyana cewa an mika wa Tinubu wasikar ne a ranar Talata, 19 ga watan Disamba, 2023.
Lalong ya bayyana cewa, bayan kammala shari’ar da aka kammala, kotun daukaka kara ta bayyana shi a matsayin zababben dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Filato ta kudu tare da umurtar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta ba shi takardar shaidar cin zabe.
Ya kuma gode wa shugaban kasar da ya nada shi minista.
A wani labarin kuma, Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2024 Na N314bn Ya Zama Doka
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya rattaba hannu kan kasafin kudin jihar na Zunzurutun Kudi Naira biliyan N314.8bn
Wannan na zuwa ne bayan wata daya kacal da majalisar dokokin jihar ta amince da shi
Kasafin kudin zai samar da tsare-tsare da gwamnati za ta yi don magance bukatun ci gaban jihar
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, a ranar Talata, ya rattaba hannu kan kasafin kudin jihar na Zunzurutun Kudi Naira biliyan N314.8bn na shekarar 2024.
Wannan na zuwa ne bayan wata daya kacal da majalisar dokokin jihar ta amince da shi.