- Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Paul Merson ya yi hasashen sakamakon wasannin gasar Premier
- Tuni wannan Hasashen ya nuna yadda wasu manyan kungiyoyin Kwallon kafa zasu Sha da kyar
- Abaya dai wannan Hasashen Bai Yiwa Wasu manyan kungiyoyin Kwallon kafa da diba
Shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Paul Merson ya yi hasashen sakamakon wasannin gasar Premier na mako na 18 da za a yi a Ingila a karshen mako.
West Ham za ta karbi bakuncin Manchester United a gasar Premier da yammacin ranar Asabar a filin wasa na London.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Abia ta Amince da Kasafin N567bn
Liverpool za ta kara da Arsenal a yammacin ranar Asabar a Anfield.
Chelsea za ta kara da Wolves a gasar Premier a waje da yammacin Lahadi.
A cewar Sportskeeda, hasashen Merson Ya Kasance kamar haka:
Crystal Palace zasu tashi cancaras daci 1-1 da Brighton
Aston Villa za ta lallasa Sheff United daci 2-0
West Ham zasu tashi kunnen doki da Man United daci 2-2
Fulham za ta zazzagawa Burnley kwalleye 3-0
Luton zasu tashi cancaras da Newcastle da ci 1-1
Tottenham za ta lallasa Everton da ci 3-1
Nottingham Forest zasu tashi da ci 1-2 da Bournemouth
Liverpool da Arsenal zasu Kece Raini Inda Wasan Zai Tashi da ci 2-2
Wolves da Chelsea zasu barje guminsu inda zasu karkare da ci 2-2
A wani labarin kuma, An Saki Sunayen Wadanda Suka Yi Nasarar Samun Aikin Dan Sanda Su 416,270
Hukumar daukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta amince da ranar 8 ga watan Janairu, 2024, a matsayin ranar da za a fara tantance wadanda suka yi nasara
Hukumar ta gargadi ‘yan takarar da suka yi nasara da su yi taka-tsan-tsan da masu damfara
Daukar ma’aikata kyauta ne ba’a Biyan ko sisi kuma za a yi la’akari da cancanta Ne kawai
Hukumar daukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta amince da ranar 8 ga watan Janairu, 2024, a matsayin ranar da za a fara tantance wadanda suka yi nasarar daukarsu aiki a matsayin Jami’an ‘yan sanda na rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a Ikechukwu Ani ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya ce hukumar ta gana a hedikwatar hukumar da ke Jabi, Abuja, inda ta dauki matakai da dama dangane da mataki na gaba na aikin daukar ma’aikata.