- Rundunar sojin Najeriya, bayan wani samame da ta kai a dajin Gundumi da ke Sokoto, ta mika wasu mutane 66 da aka ceto ga gwamnatin jihar Sokoto
- Bayan Karbar wadanda aka Ceto Daga Hannun sojoji Gwamnatin Jihar ta basu Kyautar magudan kudade
- Tuni Rundunar Sojin Tasha Alwashin cigaba da dakile Ayyukan ‘yan Ta’adda aduk Inda suke
Rundunar sojin Najeriya, bayan wani samame da ta kai a dajin Gundumi da ke Sokoto, a ranar Lahadi ta mika wasu mutane 66 da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ga gwamnatin jihar Sokoto.
Kwamandan runduna ta 8 ta Garrison, Birgediya Janar Amos Tawasimi, yayin da yake mika wadanda abin ya shafa ga gwamnatin jihar ya ce an ceto 52 daga cikin wadanda aka sace ne a ranar Juma’a, yayin da wasu 14 kuma aka ceto a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Filato Ta Yi Allah-Wadai da Hallaka Mutane 16 a Jihar
“A wani bangare na ayyukanmu na tabbatar da cewa jihar ta kasance lafiya ga mutane don gudanar da ayyukansu
“Kwanaki uku da suka wuce, mun kai hari dajin gundumi domin ceto wadannan adadin mutanen da wadannan masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su tsawon watanni.”
Ya yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake baiwa jami’an tsaro tare da tabbatar da cewa mutanensa za su ci gaba da yin abin da ake bukata.
Da yake jawabi yayin karbar wadanda harin ya rutsa da su, gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu Sokoto, ya yabawa rundunar sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro a jihar bisa kokarinsu da jajircewarsu wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“A yau wani muhimmin ci gaba ne a yakin da muke yi da ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma masu satar mutane a jihar domin jami’an tsaron mu sun yi nasarar ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su daga kauyuka da al’ummomi daban-daban a Sakkwato da sauran jihohin makwabta.
“Daga abin da muka tattara, an ceto 52 daga cikin wadanda abin ya shafa a ranar Alhamis yayin da 14 a ranar Asabar.
“Za a iya tunawa cewa, a makonnin da suka gabata an kubutar da mutane 52 da abin ya shafa bayan da sojojin mu suka fatattaki wadannan miyagun daga maboyarsu da ke dajin Tangaza a karamar hukumar Tangaza ta jihar.
A halin da ake ciki kuma a kokarinsa na tallafawa wadanda aka ceto, gwamnan ya bayar da gudummawar buhun shinkafa, gero da masara baya ga naira dubu dari ga kowannen su a yayin da yake ganawa da iyalansa.
Shima da yake jawabi, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko, wanda ya mika kayan tallafin ga wadanda abin ya shafa, ya kuma sanar da bayar da tallafin naira dubu dari ga kowannen su domin su sayi magunguna da sauran kayayyaki.
Da yake yabawa gwamnatin jihar kan tantance mutanen da lamarin ya shafa, Wamakko, wanda shi ne shugaban jam’iyyar APC a jihar, ya kuma yi alkawarin tallafa wa jami’an tsaro a kananan hukumomi takwas na gundumar Sokoto ta Gabas da motocin Toyota Hilux kowacce.
A wani labarin kuma, Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha Ya Musanta Zargin Sace Dala $6.3m
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, ya karyata rahoton da ke cewa yana da hannu wajen cire dala miliyan 6.3 daga babban bankin Najeriya CBN ba bisa ka’ida ba
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya ce ba shi da masaniya game da abin da ake cewa kan wannan Zargi na badakala
Tsohon SGF ya yi kakkausar suka da kakkausar murya, inda ya ce zarge-zargen da ake yi ba su da tushe balle makama yaukuri ne na Karya da kuma kage
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Boss Mustapha, ya karyata rahoton da ke cewa yana da hannu wajen cire dala miliyan 6.3 daga babban bankin Najeriya CBN ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Rahotanni sun bayyana cewa, wani mai bincike na musamman da shugaban kasa Bola Tinubu ya nada ya bankado wannan satar da ake zargin ta faru ne a ranar 8 ga watan Fabrairun 2023— makonni kafin zaben shugaban kasa.