- Jam’iyyar PDP ta Sanya ranar gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar biyo bayan Zaben cike Gurbi da za a yi a watan Fabrairun 2024
- PDP tace fam din tsayawa takara na Sanata ya kai Naira miliyan 3 Yayin da na Majalisun Jihohi Zai Kasance Naira miliyan 2
- Mata masu neman takara da nakasassu PWD za su biya kudin fam din nagani inaso Ne kawai
Jam’iyyar PDP ta tsayar da ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2024, domin gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar biyo bayan Zaben cike Gurbi da za a yi a watan Fabrairun 2024.
Jam’iyyar a cikin tsari da jadawalin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda babban sakataren jam’iyyar PDP na kasa Umar Bature ya fitar, ta kuma sanya ranar 28 ga watan Disamba, 2023 zuwa ranar 3 ga watan Janairu, 2024 na tsawon lokacin sayar da fom din tsayawa takara da nagani inaso.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Wasu Fursunoni Uku Sun Tsere Daga Gidan Yarin Jihar Ogun
Za a gudanar da zaben cike gurbi a ranar 3 ga watan Fabrairun 2024 a gundumar Ebonyi ta Kudu ta jihar Ebonyi; Sanatan Yobe ta Gabas ta Jihar Yobe; Gundumar Sanatan Plateau ta Arewa ta Jihar Filato; Akoko ta Arewa maso Gabas/Akoko ta Arewa maso yamma matsabar tarayya dake Jihar Ondo.
Sauran sun hada da mazabar tarayya ta Jalingo/Zorro/Zing ta jihar Taraba; mazabar Tarayya ta Surulere 1 dake Lagos; mazabar Tarayya ta Yauri/Shanga/Ngaski dake jihar Kebbi; Mazabar Chibok ta jihar Borno; Mazabar Chikun ta Jihar Kaduna; Mazabar Guma ta jihar Benue.
Bature ya ce za a kuma gudanar da tantance masu neman tsayawa takara a ranar 4 ga watan Janairu, 2024, yayin da za a gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 9 ga watan Janairun 2024.
Ya kara da cewa ranar karshe na mika sunan dan takara ga tashar zabe ta INEC za ta kasance ranar 12 ga watan Janairu, yayin da ranar karshe ta fitar da sunayen wakilan jam’iyyar a ranar 20 ga watan Janairun 2024.
Sai dai jam’iyyar ta bayyana kudin da za’a kashe na nagani inaso da fam din Tsayawa takarar majalisar dattawa da ta wakilai a kan naira 500,000 kowannen su, yayin da fam din takara ya kai naira miliyan uku da miliyan biyu.
Majalissar Dokoki an kayyade fam din nagani inaso akan Naira 100,000 yayin da kudin fam din takara ya kai N600,000.
Bature ya bayyana cewa mata masu neman takara da nakasassu (PWD) za su biya kudin fam din nagani inaso Ne kawai.
“Matasa (maza/mata) da ke kasa da shekaru 40 za su sayi fom na nagani inaso, amma tare da rangwamen kashi 50 cikin 100 akan fom na tsayawa takara,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Gwamnoni Sun ziyarci Tinubu a Legas
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da wasu gwamnonin jihohi sun ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu a gidan sa da ke Legas
Wannan dai na zuwa bayan da Shugaban kasar ya Koma jihar Legas don hutun kirsimeti
Ziyarar ta kasance ta bangirma ga Shugaban kasar da kuma tattauna Wasu batutuwa
Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da wasu gwamnonin jihohi sun kai ziyarar ban girma ga shugaban kasa Bola Tinubu a gidan sa na Bourdillon da ke jihar Legas.
Shettima da Gwamnonin sun yi wa Shugaban kasa mubayi’ar Kirsimeti.