- Yanzu haka dai wasu rahotanni dake fitowa Sun bayyana cewa wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali da tarbiyya na Ijebu Ode da ke jihar Ogun
- Tuni Hukumomin gidan yarin suka Bayyana cewa an shiga farautar fursunonin da Suka tsere
- Tserewar furusnoni ko fasa gidajen yari ba sabon abu ba ne a Najeriya
Yanzu haka dai wasu rahotanni dake fitowa Sun bayyana cewa wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali da tarbiyya na Ijebu Ode da ke jihar Ogun a kudancin Najeriya.
Tuni dai hukumomin gidan yarin suka tabbatar da tserewar fursunonin guda uku.
KARANTA WANNAN: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima, Gwamnoni Sun ziyarci Tinubu a Legas
Wannan na kunshe ne ta Cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen gyaran hali reshen jihar Ogun Victor Oyeleke ya fitar.
Kakakin ya ce fursunonin sun tsere ne ranar Asabar da tsakar dare ta hanyar tsallaka katanga.
A cewar sanarwar, tuni aka shiga farautar fursunonin – hukumomin sun ce suna da bayanansu da kuma iyalansu, suna kuma aiki da sauran hukumomi domin dawo da su cikin gaggawa.
Kazalika, sanarwar ta ce ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere yana zaman gidan yarin ne kan hukuncin fashi da makami da aka yanke masa, ɗayan kuma an ɗaure shi a gidan yarin ne kan aikata kisan kai.
Mutum na ukun kuma yana zaman gidan yari kan aikata cin zarafin lalata.
Tserewar furusnoni ko fasa gidajen yari ba sabon abu ba ne a Najeriya.
Masana kuma na bayyana damuwa kan haɗarin da ke tattare da matsalar fasa gidajen yari wanda ke bayyana irin rikon sakainar kashi da ake yi wa gidajen yarin musamman a halin rashin tsaro da dukkan sassan ƙasar ke fuskanta.
A wani labarin kuma, Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutane Bakwai, 11 Sun Bace a Afirka ta Kudu
Jami’ai sun ce an shatata ruwan sama kamar da bakin kwarya Inda aka bazama domin gano wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a wani lardin Afirka ta Kudu
Bayan afkuwar ambaliyar, an yi hasashen za a samu karin mumunar guguwa a fadin lardin
Wannan dai bashi ne karon farko da Yankin ya ke fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da bala’o’in yanayi a daidai lokacin da ake fama da yanayin zafi a duniya ba
Jami’ai sun ce an shatata ruwan sama kamar da bakin kwarya a ranar Talata Inda aka bazama domin gano wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a wani lardin Afirka ta Kudu wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla bakwai tare da bacewar wasu 11.
Ambaliyar ruwa mai nisan mita 10 (kafa 33) ta ratsa wata gundumar Ladysmith, a lardin KwaZulu Natal, inda ta lalata gidaje tare da kwashe motoci, in ji masu ceto a cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar a ranar Talata.