- A yayinda da ake cikin Jimamin hallaka mutane 10 da yan Bindiga su ka yi a Karamar Hukumar Jibiya sai ga kuma wani harin a Karamar Hukumar Faskari
- Dukkan farmakin da ‘yan bindigar Suka Kai sun Kai shine kan Jami’an tsaro na sa Kai da gwamnan Jihar ya kafa
- A yan Kwanakin Nan dai ana Kara samun Kai farmakin ‘yan Bindiga kan wadanda basu ba basu Gani ba
A yayinda da ake cikin Jimamin hallaka mutane kusan Goma da yan Bindiga su ka yi a Karamar Hukumar Jibiya sai ga kuma wani harin a Karamar Hukumar Faskari a dai jihar ta Katsinan.
Rahotanni sun nuna cewa baya ga wancan harin na Jibiya, yan Bindigar sun kuma kai wani harin a ranar Talata a karamar hukumar Faskari inda su ka kai farmakin ga mambobin kungiyar sa kai da Gwamnan jihar ya kafa.
KARANTA WANNAN: Filato: Kakakin Majalisa Abbas Ya Yi Allah-Wadai Da Sabbin Kashe-Kashen Da Aka Yi
A harin dai na Faskari ana zargin kusan duk yayan waccan kungiya abun ya shafa inda aka ce an hallaka mutane biyu Inda aka raunata Wasu daga cikin dakarun na sa kai.
Wadanda yan Bindigar suka hallaka sun hada da Hasan Abdullahi da kuma Idris Shu’aibu. Sai kuma Alhaji Abdullahi Kanta wanda a farko aka nemi shi ma aka rasa.
Dukkan su Jami’an tsaron ne na sa kai a yankin Karamar Hukumar Faskari.
Su dai yan Bindigar a jihar katsina na kara zafafa hare haren su ne musamman akan Jami’an tsaron sa kai kasancewar su ma in suka kama su ko abokan tonon sirrin su ko masu ba su haske da aka fi sani da Informa ba sa yi musu da dadi.
A wani labarin kuma,Zaben Cike Gurbi: PDP ta Sanya Ranar Gudanar da Zaben Fidda Gwani
Jam’iyyar PDP ta Sanya ranar gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar biyo bayan Zaben cike Gurbi da za a yi a watan Fabrairun 2024
PDP tace fam din tsayawa takara na Sanata ya kai Naira miliyan 3 Yayin da na Majalisun Jihohi Zai Kasance Naira miliyan 2
Mata masu neman takara da nakasassu PWD za su biya kudin fam din nagani inaso Ne kawai
Jam’iyyar PDP ta tsayar da ranar 8 ga watan Janairun shekarar 2024, domin gudanar da zabukan fitar da gwani na jam’iyyar biyo bayan Zaben cike Gurbi da za a yi a watan Fabrairun 2024.
Jam’iyyar a cikin tsari da jadawalin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar wanda babban sakataren jam’iyyar PDP na kasa Umar Bature ya fitar, ta kuma sanya ranar 28 ga watan Disamba, 2023 zuwa ranar 3 ga watan Janairu, 2024 na tsawon lokacin sayar da fom din tsayawa takara da nagani inaso.