- Gwamnan Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi alhinin rasuwar takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu
- Tuni Wasu Bayanai dake fitowa Daga Jihar Suka Bayyana cewa ana shirin rantsar da mataimakinsa Aiyedatiwa
- Kafin rasuwar Marigayin ya kasance tsayayye kuma Mai jajircewa kan al’amuran Daya Sanya a gaba
Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yi alhinin rasuwar takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.
A baya dai Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Akeredolu ya rasu.
KARANTA WANNAN: Ganduje Ya Yi Ta’aziyya Ga Iyalan Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ghali Na’Abba
Majiyoyi sun ce gwamnan ya rasu ne a ranar Laraba yana da shekaru 67.
Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a jihar ya ce ana shirin rantsar da mataimakinsa Lucky Aiyedatiwa.
Har yanzu dai gwamnatin jihar ba ta ce uffan ba kan lamarin.
Amma da yake mayar da martani kan ci gaban, AbdulRazaq, wanda shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ta hannun mai magana da yawunsa, Rafiu Ajakaye, ya bayyana Akeredolu a matsayin “babban dattijon kasa wanda ya yi tazarce a aikin gwamnati”.
“Ina mika ta’aziyyata ga kungiyar gwamnoni, gwamnati da al’ummar jihar Ondo, kungiyar lauyoyi ta Najeriya, da kuma dangin dan uwana kuma abokin aikina mai girma Olurotimi Akeredolu SAN.
“Lauya na kan gaba kuma dan siyasa mai kishin kasa, za a tuna da gwamnan saboda jajircewarsa, kishin kasa, da gudummawar da ba ta da iyaka ga ci gaban tsarin mulkin Najeriya da zamantakewar siyasa.
“Kamar yadda mutuwarsa ke da zafi a gare mu duka, muna samun ta’aziyya a cikin kyawawan abubuwan da ya gada a matsayinsa na mai gaskiya kuma mai mulki. Muna rokon Allah ya jikansa da rahama ya kuma duba iyalansa.” Sanarwar ta kara da cewa.
A wani labarin kuma, Dole Ne Mu Hada Kai Don Tabbatar Da Zaman Lafiya a Najeriya — Tinubu Ga gwamnoni
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya da Sauran gwamnatoci na da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya
Shugaban ya bayar da wani kakkausan umarni ga jami’an tsaro da su dakatar da kashe-kashen da ake yi tare da kara zage damtse wajen zakulo wadanda suka haddasa munanan abubuwan
Ya zama wajibi mu yi watsi da rabe-raben hanyoyin tarayya, jiha ko karkara. Dole ne mu dauki ci gaba a matsayin alhakin hadin gwiwa
Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatin tarayya da Sauran gwamnatoci na da alhakin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Da yake magana yayin ganawarsa da kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, a gidansa da ke Legas a ranar Talata, shugaban ya sake yin Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato.