- Gabanin hukuncin kotun koli kan rikicin gwamnan Kano, tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira ga gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf da abokin hamayyarsa, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna da su amince da hukuncin kotun kolin
- “Allah a cikin rahamarsa marar iyaka yana ba da mulki ga wanda yake so ba tare da la’akari da addininsa, kabilarsa, ko waninsa ba. Nagari da mara kyau
- Dole ne Yusuf da Gawuna su fahimci cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so
Gabanin hukuncin kotun koli kan rikicin gwamnan Kano, tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau ya yi kira ga gwamna mai ci Alhaji Abba Kabir Yusuf da abokin hamayyarsa, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna da su amince da hukuncin kotun kolin ga Duk Wanda ya Samu nasara.
Wannan dai shi ne kamar yadda tsohon gwamnan ya kuma shawarci kotun koli da ta yi gaskiya da adalci a hukuncin da za ta yanke kamar yadda kuma Allah zai hukunta su a kan ayyukansu na alkalai.
KARANTA WANNAN: Gwamnan Adamawa Ya Yi Ta’aziyya Ga Gwamnatin Ondo Bisa Rasuwar Akeredolu
“Muna fatan alkalan za su yi abin da ya dace. Idan sun yi kuskure, bari mu san cewa su mutane ne.
Malam Shekarau wanda ya ba da wannan shawara a Kano, ya bayyana cewa dole ne Yusuf da Gawuna su fahimci cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda ya so.
Sai dai ya kara da cewa yana sa ran kotu za ta yi adalci amma ya shawarci jama’a da su gane cewa alkalai ma mutane ne.
“Allah a cikin rahamarsa marar iyaka yana ba da mulki ga wanda yake so ba tare da la’akari da addininsa, kabilarsa, ko waninsa ba. Nagari da mara kyau
“Ina fata kuma ina kira ga Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna da su dauki wannan a matsayin addu’a. Su roki Allah da mafificin alkhairi a gare su. Idan kuwa ba alkhairi ba ne to su roki Allah ya musanya musu da mafi alheri.
“Shawarar da zan ba su ita ce duk wanda ya yi rashin nasara kada ya yi fushi ya zargi wani ya yi masa. Sai ya roki Allah ya canza masa abin da ya dace.
“Allah ya zaba wa Kano shugabanni da za su amfani jama’a da kuma jihar. Wannan shi ne abin da muke addu’a. Shi kaɗai ya san wanda zai baiwa kuma muna da bege cewa zai amsa addu’o’inmu.
“Batun wannan shi ne wanda muke so; wanda zai iya isarwa ko a’a ba haka lamarin yake ba ko da yake ita ce hanyar da mutane ke zaɓa da bayyana kansu daga sha’awarsu.
“Hatta alkalai, su yi aiki da abin da aka gabatar musu kuma Annabi mai tsira da amincin Allah ya gaya mana cewa alkali idan zai yanke hukunci yana da lada ko ta yaya. Idan ya yi adalci yana samun lada biyu, idan kuma ya yi ba haka ba, yana da lada guda.”
A wani labarin kuma, Gobara ta Tashi A Wani Gidan Mai Ta Raunata Ma’aikatan
Akalla mutane hudu ne suka samu raunuka daban-daban a yayin da gobara ta tashi a wani gidan mai dake Legas
Tuni aka garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa babban asibiti kafin isowar jami’an kashe gobara
Lamarin dai ya afku ana Tsaka da kokarin yadda za a Yi fasakwaurin man zuwa Wata kasa
Akalla mutane hudu ne a ranar Laraba suka samu raunuka daban-daban a yayin da gobara ta tashi a gidan man Fat Noble, wani kamfani mai zaman kansa na sayar da mai da ke Old Road, daura da Torikoh, Badagry, Legas.
NAN ya rawaito cewa ma’aikatan sun rika rarraba mai a cikin jarkoki da buhuna da misalin karfe 1.00 na safe a bayan gidan man lokacin da fashewar ta faru.