- Gwamnan Adamawa, Ahmadu Finitri, ya jajanta wa al’ummar Ondo, bayan rasuwar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu
- A Koda yaushe za a tuna da abin da ya bari na gado
- Marigayin Gwamnan dai ya rasu Yana da Shekaru 67 Wanda Rashin lafiyarsa ta Haifar da cece-ku-ce a jihar
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Finitri, ya jajanta wa al’ummar jihar Ondo, bayan rasuwar gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu.
Finitri ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a safinsa na X ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: Gobara ta Tashi A Wani Gidan Mai Ta Raunata Ma’aikatan
Ya rubuta “Ina mika ta’aziyyata ga al’ummar Jihar Ondo bisa rasuwar Gwamna Rotimi Akeredolu SAN.
“Za a tuna da abin da ya gada, kuma tunanina yana tare da iyalansa da kuma daukacin jihar Ondo a wannan mawuyacin lokaci.
Allah ya jikansa yasa ya huta.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa gwamnan jihar Ondo ya rasu ranar Laraba yana da shekaru 67.
A wani labarin kuma, An Samu Kilo 120 Na Hodar Iblis Yashe A Bakin Tekun Australia
‘Yan sandan Ostireliya sun Samu wasu abubuwa masu ban mamaki da aka yi imanin yakai fiye da kilo 120 (fam 260) na hodar iblis a Bakin teku
Yan sanda sun bukaci mutane da su kai rahoton duk wani kunshin da ake tuhuma
Wannan lamari dai ya jefa mazauna Yankin Cikin firgici da damuwa don Gudun me kaje yazo
‘Yan sandan Ostireliya sun fada a ranar Laraba cewa suna duba bakin teku bayan samun wasu abubuwa masu ban mamaki da aka yi imanin yakai fiye da kilo 120 (fam 260) na hodar iblis Yashe a lokacin Kirsimeti.
‘Yan sanda sun ce an gano rukunin farko na sinkin mai nauyin kilo 39 da ake zargin hodar Iblis ne a ranar Juma’a a kusa da bakin tekun Magenta da ke arewacin Sydney.