- Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu, ta tarbi jaririn farko na bana, Boluwatife Johnson, da aka Haifa a asibitin kasa
- Misis Tinubu ta bukaci masu fada a ji a kasar nan da su hada kai da gwamnati don inganta harkar kiwon lafiya a kasar, domin gwamnati ba za ta iya yin shi ita kadai ba
- Ya kamata iyaye mata masu shayarwa su kula da jariransu yadda ya kamata, su tabbatar an yi musu alluran rigakafi a lokacin da ya dace
Uwargidan shugaban kasa, Remi Tinubu, a ranar Litinin, ta tarbi jaririn farko na bana, Boluwatife Johnson, da aka Haifa a asibitin kasa da ke Abuja.
An haifi Boluwatife da misalin karfe 12.03 na safe ranar 1 ga watan Janairu.
KARANTA WANNAN: Ba A Samu Asarar Rai Ba A Gobarar Ofishin Fasaha Da Al’adu Ta Kasa – Jami’i
Misis Tinubu ta bukaci masu fada a ji a kasar nan da su hada kai da gwamnati don inganta harkar kiwon lafiya a kasar, domin gwamnati ba za ta iya yin shi ita kadai ba.
“Ina kira ga iyaye mata masu shayarwa da su kula da jariransu yadda ya kamata, su tabbatar an yi musu alluran rigakafi a lokacin da ya dace, su rika shayar da jarirai nonon uwa zalla tare da samar musu da abinci mai gina jiki da lafiyayyen yaye domin ci gaban kwakwalwarsu.
“Ya kamata iyaye mata masu zuwa su rika kula da mata masu juna biyu da haihuwa da muhimmanci, su kula da tsaftar gida a gidajensu, su yi wa jariransu rijista da hukumar kidaya ta kasa da kuma yin kokarin shigar da su makaranta a lokacin da suka dace,” in ji ta.
Uwargidan shugaban kasar ta kuma bukaci mata da su san halin da suke ciki na kanjamau.
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: Kakakin Majalisar Dokokin Ribas Mai Biyayya Ga Gwamna Fubara Ya Yi Murabus
Yanzu haka dai bangaren kakakin majalisar dokokin Ribas, Edison Ehie, ya yi murabus daga mukaminsa da kuma zama dan majalisar
Tuni dai wannan lamari na Murabus din Kakakin Majalisar ya girgiza Gwamnan
Murabus din kakakin Majalisar na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya tsoma baki a rikicin siyasar da ya dabaibaye jihar
Bangaren kakakin majalisar dokokin jihar Ribas, Edison Ehie, ya yi murabus daga mukaminsa da kuma zama dan majalisar.
Murabus din Edison na kunshe ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 29 ga watan Disamba, 2023, kuma ta sa mu rattaba hannu.