Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu barayin mota guda uku tare da kwato motocin da suka sace a Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Kaduna.
Karanta nanYan Sanda Sun Kama Masu Satar Katifun Makaranta A Jigawa
Hassan ya ce a ranar 23 ga watan Disambar 2023 da misalin karfe 06:00 ne jami’an da ke hedikwatar shiyya ta birnin Zariya suka yi aiki da sahihan bayanai, lamarin da ya kai ga cafke wadanda ake zargin a Agoro-Tudun Wada, Zariya.
Ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin mai shekaru 28 Hayin Baki dan garin Birnin Gwari yana da wata mota kirar Toyota Corolla da aka sace mai lamba Kano GWL 188 TT.
Hassan ya ce a wani labarin makamancin haka, jami’an sashen Sabon Gari Zariya a wannan rana, da misalin karfe 18:30, sun kama wani da ake zargi, suka kuma gano motarsa kirar Toyota Corolla LE 2003 mai launin toka.
Wanda ake zargin ya amsa laifin satar motar ne a cikin garin Kaduna kuma ya kawo ta Zaria domin ya sayar.
Ya ce wanda ake zargin sojan da aka kora ne da ya shahara wajen satar mota da sauran munanan ayyuka a Benin da Kaduna da kuma Zariya.
Hakazalika, a ranar 27 ga Disamba, 2023, jami’an mu na sashin Sabon Gari Zariya sun kama wani da ake zargi na Graceland Zaria da wata babbar mota kirar Toyota Hilux da aka sata mai lamba Jigawa GML 40 AG.
A wani labarin kumaYan Sanda Sun Kama Masu Satar Katifun Makaranta A Jigawa
Tun daga yanzu an gano wanda ya mallaki motar da aka sace, na titin Aliyu Mohammed Unguwan Kaduna.
Hassan ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Audu Ali, ya yabawa ‘yan sandan bisa nasarar da aka samu, inda ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa wajen hana masu aikata laifuka a jihar duk wani wurin aiki.
Ya yi kira ga jama’a da su rika baiwa jami’an tsaro bayanai masu inganci a kan wadanda ake zargi a yankinsu domin a gaggauta mayar da martani.