- Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA hadin gwiwa da takwararta ta jihar katsina SEMA sun rarraba kayayyakin tallafi ga mutane dubu 9000
- An zaɓo mutanen ne a ƙananan hukumomin da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa
- Ana saran kayayyakin tallafin zasu rage radadin da wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA hadin gwiwa da takwararta ta jihar katsina SEMA sun rarraba kayayyakin tallafi ga mutane dubu 9000 a faɗin ƙananan hukumomi 22 na jihar Katsina.
Kayayyakin da aka rarraba sun haɗa da kekunan ɗinki, da injin feshi da maganin feshi, da kuma irin shinkafa da Waken Suya.
KARANTA WANNAN: An Kaddamar da Littafin Tarihin Wanda Ya Fara Kai Injin Nika Jihar Katsina
Wannan kayayyaki ya kasance cikon kashi na farko ne da aka fara rabawa a shekarar 2023, sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da aka fuskanta a shekarar 2022 a Katsina.
Sannan an rarraba kayayyakin tare fatan cewa, nan gaba kaɗan za’a ƙara rarraba kayayyakin domin amfanin al’ummar jihar Katsina.
Taron ya wakana a farfajiyar ofishin magajin garin Katsina kusa da Babban masallacin Katsina.
Da take jawabi jim kaɗan bayan rarraba kayayyakin ga mata da maza, wakiliyar hukumar NEMA Hajiya Ummuna Ahmed, tace an bada kayayyakin ne ga mutane sama da dubu 9,000 a faɗin ƙananan hukumomin Katsina, domin rage masu raɗaɗin iftila’in ambaliyar ruwa da ya shafe su.
Hajiya Ummuna Ahmed ta ƙara da cewa, kekunan ɗinkin an baiwa mata ne kaɗai, ya yinda maza da wasu matan aka basu kayayyakin feshi da buhun shinkafa, wanda har da masu tsananin bukata suma an sanya su a bada tallafin.
A nata jawabin, Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina Hajiya Binta Hussaini Ɗangani, tace an zaɓo mutanen ne a ƙananan hukumomi 22 da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa, ƙarƙashin wani shirin bada tallafi da NEMA ta ɓullo da shi na bada tallafi ga waɗanda iftila’in ruwa ya shafa.
Hajiya Binta Hussaini Ɗangani tace an rarraba kayayyakin ne da suka haɗa da injin feshi da maganin feshi da irin shinkafa da waken suya, wanda aka bayar domin taimakawa mutane wajen noma wa.
DIMOKURADIYYA TV ta jiyo Dan Gani na cewa ‘Wannan tallafi da aka bayar cikon kashi na biyu ne da ɗaya da NEMA ta bayar haɗin gwiwa da jihar Katsina. Haka nan,muna saran ganin wani tallafin a wannan shekara ta 2024″.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Tarayya Ta Tsawaita Wa’adin Rajistar Aikin Hajjin 2024
Gwamnatin tarayya ta amince da tsawaita wa’adin rijistar aikin hajjin shekarar 2024
Karin wa’adin ya biyo bayan damuwar da masu ruwa da tsakai suka Nuna kan lamarin
NAHCON ta jajirce wajen ganin an shawo kan matsalolin masu ruwa da tsaki don kawar da duk wani cakas na aikin hajji
Gwamnatin tarayya ta amince da tsawaita wa’adin rijistar aikin hajjin shekarar 2024 da maniyyata za su yi.
Madam Fatima Usara, mataimakiyar daraktar hulda da jama’a ta hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Talata.