- Yanzu haka dai a jihar Katsina an ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Dan kasuwa marigayi Alhaji Sodangi
- Zuwan injin Nika jihar ya saukakawa mata wajen nika hatsi a wancan lokacin
- Kafin zuwan injin Nika mata suna nika hatsi da duk abunda ya samu a Dutsen Nika na hannu
A jihar Katsina an ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Dan kasuwar nan marigayi Alhaji Sodangi.
Wannan na zuwa ne ya yin da zuri’ar banu Abdurahman Maikeke wadda reshe ce, ta kungiyar zuri’ar banu hambali dake unguwar Alkali Katsina, sun ƙaddamar da littafin rayuwar mariyagayi Alhaji Sodangi mai suna “The Dove” wanda da Hausa ake kira da “Tantabara”.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Tarayya Ta Tsawaita Wa’adin Rajistar Aikin Hajjin 2024
Shi dai Alhaji Sodangi shi ne mutum na farko a tarihin jihar Katsina, da ya kai injin niƙa jihar.
Littafin ya kasance Wanda Alhaji Yahayya Garba Mahmood ya rubuta shi a kan rayuwar Alhaji Sodangi wanda ya rasu fiye da shekaru ashirin da suka Gabata.
Taron ya samu halartar manyan baki ciki da wajen Jihar Katsina da su ka hada da Ministar Al’adu Hannatu Musawa, da Ministan gidaje Ahmed Ɗangiwa da sauransu.
Tun farko a nasa jawabin na maraba Barista Muntari Ibrahim Wakilin shugaban taro yace an rubuta littafin ne a harshen turanci inda aka saukaka shi, don fahimta ga makaranta.
A wani labarin kuma,Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Bilyan Ɗari Don Ciyar Da Ɗalibai
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa an ware Naira biliyan 100 a kasafin kudin shekarar 2024 don shirin ciyar da dalibai
Wannan tanadin zai zama abin kara kuzari don karfafa halartar makarantu da kuma rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta
Shirin wanda a baya aka dakatar da shi a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, yanzu zai koma karkashin ma’aikatar ilimi
Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2024 ya hada da ware Naira biliyan 100 na shirin ciyar da dalibai.
Ya bayyana hakan ne a yayin rattaba hannu kan kudirin kasafin kudi na shekarar 2024 da ya zama doka a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.