- Jami’an Hukumar EFCC, sun kai samame babban ofishin kamfanin Dangote dake Legas
- Jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan wasu kudade
- Wannan dai na zuwa ne bayan da Dangote ya rikito da ga wanda yafi kowa kudi a nahiyar Afirka
Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Alhamis, sun kai samame babban ofishin kamfanin Dangote dake Legas.
Kamar yadda shafin jaridar TheCable ya rawaito, jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan kudaden da aka ware wa kamfanin a zamanin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.
KARANTA WANNAN: Tsohon Kocin Golden Eaglets Ya Rasu
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ki cewa komai kan ci gaban.
Sai dai wani ma’aikacin Dangote ya tabbatar da cewa jami’an EFCC na nan a babban ofishin kamfanin.
“Sun bukaci a ba su takardu kan hada-hadar kudi da CBN,” in ji ma’aikacin.
A wani labarin kuma, Har Yanzu Nine Shugaban Jam’iyya Na Jiha – Adams Ga PDP
Shugaban jam’iyyar PDP da aka dakatar a jihar Ondo ya ce har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar
Wannan na zuwa ne bayan jam’iyyar reshen jihar ta dakatar da shugaban Jam’iyyar a ranar Talata bisa zargin cin amanar jam’iyyar
Dakatarwar an yi ta ne domin masu hannu da shuni su aiwatar da mugun nufinsu da ake zargin su da shi na zaben zaben cike gurbi a watan Fabrairu
Shugaban jam’iyyar PDP da aka dakatar a jihar Ondo ya ce har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar.
A cewar shugaban rigimar, dakatarwar da ake yi masa ba za ta tsaya ba, yana mai jaddada cewa siyasa ce kawai.