Ma’aikatan Najeriya na sa ran karin mafi karancin albashi kafin Maris – Shugaban NLC
Shugaban kungiyar Kwadago ta kasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a kammala tattaunawa kan sabon mafi karancin albashi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago kafin watan Maris na wannan shekara.
Da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da manema labarai a ranar Alhamis, Ajaero ya ce, “Gwamnatin tarayya ta rubuta wasika ta bukaci kungiyoyin kwadago da su bayyana sunayen mu ga sabon kwamitin mafi karancin albashi da za a kafa.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton karancin ruwa a bariki
“Tun a shekarar da ta gabata ne aka mika wa gwamnati jerin sunayen kuma sai da aka kafa kwamitin ne a yanzu muka shiga tattaunawa da gwamnati a matsayin kungiya domin mu amince da shi.
“Mafi karancin albashin da ake da shi zai kare a watan Maris na wannan shekara, don haka muna fatan za mu iya kammala shawarwarin karin mafi karancin albashi kafin Maris.”
Da yake magana kan kyautar albashin da gwamnatin tarayya ta baiwa ma’aikatan Najeriya, ya bayyana cewa wata daya kacal aka biya, yana mai cewa, “Ya kamata a sako ma’aikata duka a karshen wannan shekaran Janairu.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Yobe ta Soke Lasisin Makarantun Ƴan Kasuwa
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka yada cewa iyalan sojoji a hedikwatar 14 na bariki sun kasa yin girki a ranar sabuwar shekara saboda karancin ruwa a barikin.
Mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar Laftanar Omale Innocent Prince, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce batun gyaran ruwa a barikin ya kasance kalubale domin a baya an yi kokarin shawo kan lamarin.