- Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada wasu manyan daraktoci shida a hukumar NPA da NIMASA
- Shugaban kasar ya amince da nadin ne tare da cikakken imani cewa “sabbin wadanda aka nada za su aiwatar da aikinsu cikin gaggawa da kuma inganci
- Ana sa ran sabbin wadanda aka nada za su sauya “tattalin arzikin Najeriya zuwa ga samar da ayyukan yi
Shugaban Kasa Bola Tinubu ya nada wasu manyan daraktoci shida a hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya da kuma hukumar kula da harkokin jiragen ruwa ta Najeriya.
Dukkan hukumomin biyu suna karkashin Ma’aikatar Ruwa da Tattalin Arzikin Ruwa ta Tarayya.
KARANTA WANNAN: DA Dumi-Dumi: Jami’an EFCC sun Mamaye Ofishin Kamfanin BUA
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar mai taken, ‘Shugaba Tinubu ya nada sabbin daraktocin gudanarwa a hukumomi da ke karkashin ma’aikatar kula da harkokin ruwa da tattalin arzikin ruwa ta tarayya.
A NPA, Tinubu ya nada Vivian Edet a matsayin Babbar Daraktar, Kudi da Gudanarwa; Olalekan Badmus a matsayin Babban Darakta mai kula da harkokin ruwa da ayyuka da kuma Ibrahim Umar a matsayin Babban Darakta, Injiniya da Fasaha.
A NIMASA, ya nada Jibril Abba Babban Daraktan, Ma’aikatan Maritime Labour and Cabotage Services; Mista Chudi Offodile Babban Daraktan Kudi da Gudanarwa da Fatai Adeyemi Babban Daraktan Ayyuka.
A cewar Ngelale, Shugaban kasar ya amince da nadin ne tare da cikakken imani cewa “sabbin wadanda aka nada za su aiwatar da aikinsu cikin gaggawa da kuma inganci kan aikinsu na hadin gwiwa don samar da yanayin da ake bukata don bunkasa gudummawar bangaren tattalin arziki ruwa ga GDP na kasar.”
Tinubu ya kuma sa ran sabbin wadanda aka nada za su sauya “tattalin arzikin Najeriya zuwa ga samar da ayyukan yi da hada kai wanda zai samar da sabuwar dama ga daukacin ‘yan Najeriya bisa ga tsarin sabunta bege, karkashin jagorancin ministan harkokin ruwa da tattalin arziki, Adegboyega Oyetola. ”
A wani labarin kuma, Emefiele: EFCC ta Kai Wani Simame A Babban Ofishin Dangote
Jami’an Hukumar EFCC, sun kai samame babban ofishin kamfanin Dangote dake Legas
Jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan wasu kudade
Wannan dai na zuwa ne bayan da Dangote ya rikito da ga wanda yafi kowa kudi a nahiyar Afirka
Jami’an Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Alhamis, sun kai samame babban ofishin kamfanin Dangote dake Legas.
Kamar yadda shafin jaridar TheCable ya rawaito, jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun gudanar da bincike kan kudaden da aka ware wa kamfanin a zamanin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya CBN.