- Wata kotun Area I ta Kabusa da ke Abuja ta bayar da umarnin a tsare wani dan haya
- Alkalin kotun ya bayar da umarnin ne bayan ya saurari karar wanda ake kara
- Tuni dai idon dan hayar ya raina fata kafin ya gane Shayi Ruwa ne
Wata kotun Area I ta Kabusa da ke Abuja ta bayar da umarnin a tsare wani dan haya mai suna Chris Okoye mai shekaru 44 bisa laifin dukan mamallakin gidan da yake hayar.
Alkalin kotun, Malam Abubakar Sadiq, ya bayar da umarnin ne bayan ya saurari karar wanda ake kara.
KARANTA WANNAN: Fiye da mutane 240 Sun Bace Bayan Afkuwar Wata Mummunar Girgizar Kasar a Japan
Ana tuhumar wanda ake tuhuma da ke zaune a 2A Niger Avenue villa nova, Apo da laifin hada baki, tsoratarwa, karfi, kai hari da kuma haddasa rauni.
Sai dai wanda ake karar ya musanta zargin da ake masa.
Tun da farko Mai gabatar da kara, O.S. Osho ya shaida wa kotun cewa mamallakin gidan da wanda ake zargin yake hayar yake ciki, Mista Ochengele Isaac, ya kai karar ofishin ‘yan sanda na Apo a ranar 3 ga watan Janairu.
Ya ce wanda ake kara da ‘ya’yansa biyu da Gideon a yanzu haka sun lakadawa mai gidan duka tare da raunata shi.
Osho ya ce ‘ya’yan wanda ake kara guda biyu da Gideon suna hannunsu a yanzu.
Sadiq ya dage sauraron karar har zuwa ranar 16 ga watan Janairu domin sauraren karar.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Nasarawa Ta Yiwa Fursunoni 14 Afuwa
Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rattaba hannu kan sakin fursunoni 14 da aka zabo daga sassa shida na gidajen yarin jihar
“A koyaushe ina bakin ciki idan na zo gidajen yari na ga fuskokin mutane masu hazaka
An shawarci wadanda aka yiwa afuwar da su kasance masu halin kirki kuma su nuna kyakykyawan misali domin gwamnati ta zage damtse wajen sakin wasu fursunoni
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, a ranar Alhamis ya rattaba hannu kan sakin fursunoni 14 da aka zabo daga sassa shida na gidajen yarin jihar.
Hakan dai ya yi dai-dai da yadda tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya ba shi ikon yin amfani da shi.