- Hukumar EFCC ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin da babbar kotun birnin tarayya ta yanke na bayar da diyyar Naira miliyan 100 ga tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Wannan na zuwa ne bayan da Alkalin kotun ya bayar da diyyar Naira miliyan 100 ga Emefiele da aka dakatar a kan gwamnatin tarayya da kuma EFCC
- EFCC ta ce an tsare tsohon shugaban CBN din ne da wata doka mai inganci
A ranar Litinin ne hukumar EFCC ta bayyana rashin gamsuwarta da hukuncin da babbar kotun birnin tarayya ta yanke na bayar da diyyar Naira miliyan 100 a kan tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.
Kakakin Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC, Dele Oyewale, shine wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Kotu ta Ci Tarar Gwamnatin Tarayya N100m Saboda Take Hakkin Emefiele
Kakakin na EFCC ya bayyana cewa hukumar za ta daukaka kara kan hukuncin nan take.
Oyewale ya ce a ranar Litinin mai shari’a O.A Adeniyi, ya ci tarar hukumar EFCC bayan ta yanke hukuncin cewa tsare Emefiele da ta yi a kan bincikensa tauye hakkinsa ne na ‘yanci.
“Shawarar ta gaza fahimtar cewa an tsare tsohon shugaban CBN ne da wata doka mai inganci, saboda haka hukumar za ta tunkari kotun daukaka kara ta ajiye shi a gefe.” Inji shi.
Idan dai za ku tuna a baya Adeniyi ya bayar da diyyar Naira miliyan 100 ga Emefiele da aka dakatar a kan gwamnatin tarayya da kuma EFCC bisa tauye masa hakkinsa.
Emefiele ya ja kunnen Gwamnatin Tarayya da Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya da kuma Hukumar EFCC don aiwatar da muhimman hakkokinsa na rayuwa, ’yancin kansa, sauraron shari’a da ’yancin motsi.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: An Umarci Betta Edu Ta Kai Kanta Zuwa Hedikwatar EFCC
An umarci dakatacciyar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara Dakta Betta Edu da ta kai kanta zuwa hedikwatar hukumar EFCC
Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Ministar kan badakalar zunzurutun kudi Naira miliyan 585
Hakan ya biyo bayan
Gayyatar da EFCC ta yi wa ministar bisa bin umarnin Tinubu na a gudanar da cikakken bincike da ya kunshi ayyukanta a ma’aikatar
An umarci dakatacciyar ministar harkokin jin kai da yaki da fatara Dakta Betta Edu da ta kai kanta zuwa hedikwatar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da ke Jabi, Abuja a ranar Talata, 9 ga watan Janairu.
A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Edu kan badakalar zunzurutun kudi Naira miliyan 585.