- Super Eagles sun tashi zuwa birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire, domin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2024
- Wannan na zuwa ne bayan da tawagar ta isa Legas daga Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Talata
- Wasan farko na Najeriya shine wanda zasu barje guminsu da Equatorial Guinea a filin wasa na Alassanne Quattara
Super Eagles sun tashi zuwa birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire, domin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2024.
‘Yan wasan da jami’ansu wadanda suke sanye da kayan gargajiya na Afirka, sun bar filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas zuwa Abidjan da safiyar Ranar Laraba.
KARANTA WANNAN: Zaben Gwamnan Abia: Kotun Koli Ta Yi Wani Hukunci A Karar da PDP ta Shigar
Tawagar ta isa Legas daga Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Talata.
Kungiyar Jose Peseiro ta shafe mako guda a Abu Dhabi don kammala dabarun buga Wasan AFCON.
Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ne ya shirya musu liyafar cin abincin dare a daren ranar Talata.
Zakarun Afirka sau uku za su kasance a otal din Pullman da ke Abidjan.
Wasan farko na Najeriya shine da Nzalang Nacional ta Equatorial Guinea a filin wasa na Alassanne Quattara, Ebimpe, ranar Lahadi.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Kotu ta Tasa Keyar Tsohon Minista Gidan Yarin Kuje Kan Zargin Damfara
Yanzu haka dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan wutar lantarki da karafa
Hakan ya biyo bayan gurfanar dashi da EFCC tayi kan wasu zarge
A lokacin Tsohon ministan aka samu tsaikon aikin Wutar Lantarki ta Mambilla
Yanzu haka dai wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a ranar laraba ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye zuwa gidan gyaran hali da tarbiyya na Kuje da ke Abuja.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gurfanar da tsohon ministan a gaban kuliya bisa zarge-zargen damfara a aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.