- A ci gaba da kokarin dakile karuwar barkewar gobarar a gidaje, gwamnatin Bauchi ta sayo sabbin motocin kashe gobara guda 4
- Gwamnan ya Jaddada Kudurin sa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a domin amdanin kowa
- An yi hakanne Domin karfafawa Hukumar kashe gobara ta jihar tare da kayan aikin kashe gobara na zamani don ayyuka masu inganci
A ci gaba da kokarin dakile karuwar barkewar gobarar a gidaje, gwamnatin jihar Bauchi ta sayo sabbin motocin kashe gobara guda 4 ga hukumar kashe gobara ta jihar.
An yi hakanne Domin karfafawa Hukumar kashe gobara ta jihar tare da kayan aikin kashe gobara na zamani don ayyuka masu inganci da ayyukan ceto.
KARANTA WANNAN: Super Eagles Ta Tashi Zuwa Abidjan Don Buga Wasan AFCON 2024
A wajen duba kayan aikin da aka gudanar a ranar Talata a hedikwatar hukumar kashe gobara ta jiha, kwamishinan ma’aikatar ayyuka da sufuri Alh. Ibrahim Gambo Galadima ya ce sun kai ziyarar ne domin sanin halin da manyan motocin ke ciki.
Ya nanata kudirin gwamnatin Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a domin amfanin al’ummarta.
Ya kara da cewa, gwamnati ta sayo sabbin motocin kashe gobara guda 4 tare da gyara wasu guda hudu da nufin magance kalubalen rashin tallafin kayan aiki ga jami’an kashe gobara a kananan hukumomin.
Ibrahim Gambo Galadima ya bayyana cewa Gwamna Bala Muhammad ya amince da rabon sabbin Motocin zuwa gidajen kashe gobara na Ningi, Alkaleri, Bauchi da Zaki da kuma wadanda aka gyara zuwa kananan hukumomin Toro, Dass, Darazo da Misau.
Tun da farko a nasa jawabin, Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Bauchi Engr. Bala Abubakar Garba ya ya bawa kwamishinan bisa wannan ziyarar bazata da kuma Gwamnati bisa baiwa hukumar kashe gobara ta jiha kayan aikin.
Daraktan ya yi amfani da kafafen yada labarai wajen fadakar da mutane wajen tunkarar abubuwa masu hadari da ka iya haifar da barkewar gobara, tare da sanya matsin lamba kan ayyukan kashe gobara a jihar.
Kwamishinan ya samu rakiyar babban sakataren ma’aikatar Alh. Abubakar Usman Misau da Daraktan Kudi da Akanta Alh. Haladu Akuyam kamar yadda yake kunshe cikin wata sanarwa da Muhammad Sani Yunusa Jami’in yada labarai ya fitar.
A wani labarin kuma, Zaben Gwamnan Abia: Kotun Koli Ta Yi Wani Hukunci A Karar da PDP ta Shigar
Kotun koli ta yanke hukunci a karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Okey Ahiwe suka shigar
Lauyan ya yi zargin cewa an kori wakilin PDP ne a cibiyar tattara sakamakon zabe don haka ba a wajabta kwafin sakamakon kamar yadda doka ta tanada ba
Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC da wasu daban-daban sun kalubalanci nasarar Gwamnan mai ci a kotu
Kotun koli a ranar laraba ta yanke hukunci a karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna Okey Ahiwe suka shigar na neman a soke zaben Alex Oti a matsayin gwamnan jihar Abia.
Mai shari’a John Inyang Okoro ya kebe hukuncin har zuwa ranar da za a sanar da bangarorin bayan da zasu yanke hukumcinsu na karshe.