- Hukumar gudanarwar Jami’ar ATBU, ta bullo da wata takardar rantsuwa da ta tilasta wa dalibai kada su shiga duk wata zanga-zanga
- Matakin da mahukuntan Jami’ar suka dauka ya biyo bayan wata zanga-zangar da dalibai suka yi a baya-bayan nan sakamakon kisan wani dalibi
- ATBU, ta ce makarantar ta haramta Duk wata zanga-zangar da ba ta da izini
Hukumar gudanarwar Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ATBU, ta bullo da wata takardar rantsuwa da ta tilasta wa dalibai kada su shiga duk wata zanga-zanga.
Wakilinmu ya samu labarin cewa matakin da mahukuntan makarantar suka dauka ya biyo bayan wata zanga-zangar da dalibai suka yi a baya-bayan nan sakamakon kisan da aka yi wa Joseph Agabaidu, dalibin sashen nazarin Kasa.
KARANTA WANNAN: Daukar Aikin ‘Yan Sanda: An Tantance Masu Neman Aiki 22K a Bauchi
Joseph, wanda ya fito daga karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi amma yana zaune a jihar Benue, shi ne babba a cikin ‘yan uwansa hudu da ke karatu a Jami’ar ATBU, Bauchi.
An caka masa wuka a ranar 2 ga watan Disambar shekarar 2023, yayin da yake kokarin kwato jakar budurwarsa daga hannun wadanda suka kwace mata a baya.
Mummunan lamarin ya afku ne a kusa da kasuwar Yelwan Tudu da ke unguwar Yelwa, wani yanki da ke wajen birnin Bauchi, da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Asabar.
Daily Post ta tuno da mahukuntan makarantar, su ma a wani mataki na kaucewa ta’azzarar lamarin ko kuma wasu abubuwan da ba a taba tsammani ba, nan take suka rufe makarantar a ranar 3 ga watan Disambar shekarar 2023, na tsawon mako guda na farko amma daga baya suka tsawaita lokacin da zai ci gaba da aiki har zuwa ranar 7 ga watan Janairun 2024
Wani kwafin fom din da aka fitar a ranar Litinin ya nuna cewa ya fito ne daga sashin ilimi da ke ofishin magatakardar makarantar mai lambar: ATBU/REG/ADM/24 zuwa ranar 21 ga watan Disambar 2023.
Fom din mai taken “RANTSUWA DA KYAKKYAWAR DABI’A” kamar yadda aka bayyana a daya daga cikin sakin layi na cewa “Na kara daukar alkawari ba zan shiga duk wata zanga-zanga a kowace harabar Jami’ar ba.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa ana sa ran daliban daya bayan daya za su sanya hannu kan fom din sannan su mikawa hukumar gudanarwa bayan an dawo da su.
Sannan kuma daliban za su yi alƙawarin “ba za su shiga cikin yin amfani da miyagun ƙwayoyi ba kamar yadda aka faɗa a cikin Littafin Jagoran ɗalibai.
“Hakanan, za su kuma ba Jami’ar, rahoton likita na gwajin cutar siga a kan dawowar su a ranar 8 ga watan Janairu, 2024.
Ya kara da cewa “Na yi alkawarin zama masu halin kirki da kuma shirye-shiryen bin ka’idoji da dokokin da aka gindaya na tafiyar da daliban jami’ar,” in ji shi.
Fom din ya kuma nuna cewa daliban za su sanya hannu a wasu sassan fom din da ke cewa: “Idan, ta kowace hanya, an same ni na saba wa wani sakin layi da aka ambata a sama, zan dauki nauyin hukuncin da ya dace wanda Gudanarwar Jami’ar za ta sadu da ni.”
Haka kuma ana bukatar daliban su rubuta: suna, lambar rajista, matakin ajin Karatun su, sashen, tsangaya, lambar GSM, sa hannunsu da kwanan wata da ranar iyayensu ko waliyyi, yayin da shi ma shugaban sashen zai rubuta sunansa da sa hannun sa tare da kwanan wata.
Sai dai da aka tuntubi Daraktan yada labarai na Jami’ar ta ATBU, Zailani Bappa ya ce makarantar ta haramta zanga-zangar da ba ta da izini Ne kawai.
“Hukumar gudanarwa tana adawa da zanga-zangar da ba ta da izini kawai saboda babu wata doka da ta ba wa dalibai damar shiga kowace zanga-zangar ba tare da izinin ‘yan sanda ba,” in ji shi.
A wani labarin kuma, ‘A Umarci Matata Ta Bar Gidana’, Wani Magidanci Ya Roki Kotu
Wani dan kasuwa mai suna Musa Habeeb ya roki wata kotun Upper Area da ta umurci matarsa Mulikat Shuaibu ta bar masa gidansa
Mai karar ya shaida wa kotun cewa ya saki matarsa tun watanni uku da suka wuce amma ta ki barin gidansa
An bukaci mai kara zai biya Naira dubu N100,000 na kayan jarirai na cikin da matarsa ke dauke da shi
Wani dan kasuwa mai suna Musa Habeeb ya roki wata kotun Upper Area dake Kubwa a Abuja da ta umurci matarsa Mulikat Shuaibu ta bar masa gidansa.
Habeeb ya shaida wa kotun cewa ya saki Mulikat Shuaibu tun watanni uku da suka wuce amma ta ki barin gidansa.