- Kimanin mutane 22,000 ne suka mika takardar neman aiki da ake ci gaba da daukar ma’aikata ‘yan sanda Bauci
- Babu wani wanda ya cancanta da za a bar shi ba tare da an tantance ba muddin ya mallaki dukkan takardun da ake bukata
- Wuraren aikin tantancewar ya hada da hukumomin gwamnati daban-daban dan ganin dukkan masu nema sun samin saukin wajen tantancewar
Kimanin mutane 22,000 ne suka mika takardar neman aiki da ake ci gaba da daukar ma’aikata ‘yan sanda a Najeriya a jihar Bauchi.
Wadanda suka nema wadanda suka fito daga kananan hukumomi 20 na jihar, a halin yanzu ana ci gaba da tantance su a makarantar horar da ‘yan sanda da ke Bauchi.
KARANTA WANNAN: ‘A Umarci Matata Ta Bar Gidana’, Wani Magidanci Ya Roki Kotu
Aikin tantancewar ya hada da hukumomin gwamnati daban-daban da suka hada da hukumar kula da aikin ‘yan sanda, hukumar kula da dabi’u ta tarayya, ma’aikatar harkokin ‘yan sanda, ofishin shugaban ma’aikata na jihar Bauchi, hukumar ma’aikata ta jiha, da kuma sashen horar da ‘yan sanda.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta ba da rahoton cewa tantancewar ta ƙunshi kimanta tsayi da ma’aunin ƙirji da duban likita na ɗan lokaci don tantance yanayin lafiyar masu neman a shirye-shiryen horo na gaba bayan sakin sunaye.
Da yake zantawa da manema labarai a wurin da aka gudanar da atisayen, mataimakin shugaban hukumar ‘yan sanda, Angulu Kadiri, ya ce an fara gudanar da atisayen ne a ranar Litinin da ta gabata, kuma an samu ci gaba sosai ba tare da tangarda ba.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a kammala tantancewar kamar yadda aka tsara, yana mai jaddada cewa babu wani wanda ya cancanta da za a bar shi ba tare da gangan ba idan ya mallaki dukkan takardun da ake bukata.
Kadiri ya yaba da goyon baya da hadin kai da aka samu daga gwamnatin jihar Bauchi da rundunar ‘yan sandan jihar a duk tsawon wannan atisayen.
Akan lambar da za a dauka aiki a jihar Bauchi ya ce, “Abu daya da ke da tabbas shi ne jihar Bauchi za ta samu adadin da aka ware mata. Kowacce jiha tana da lambar da za a ɗauka; Jihar Bauchi dai ba ta ke ba.”
A wani labarin kuma, Gwamnatin Bauchi ta Sayo Sabbin Motocin Kashe Gobara Guda Hudu
A ci gaba da kokarin dakile karuwar barkewar gobarar a gidaje, gwamnatin Bauchi ta sayo sabbin motocin kashe gobara guda 4
Gwamnan ya Jaddada Kudurin sa na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a domin amdanin kowa
An yi hakanne Domin karfafawa Hukumar kashe gobara ta jihar tare da kayan aikin kashe gobara na zamani don ayyuka masu inganci
A ci gaba da kokarin dakile karuwar barkewar gobarar a gidaje, gwamnatin jihar Bauchi ta sayo sabbin motocin kashe gobara guda 4 ga hukumar kashe gobara ta jihar.
An yi hakanne Domin karfafawa Hukumar kashe gobara ta jihar tare da kayan aikin kashe gobara na zamani don ayyuka masu inganci da ayyukan ceto.