- A halin yanzu dai shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan Ribas Simi Fubara
- Zuwan nasa bai rasa nasaba da rikicin siyasar da ya barke tsakanin gwamnan da ministan birnin tarayya, game da mulkin jam’iyyar PDP a jihar
- Wannan ya biyo bayan kara tsanani rikicin Siyasar jiyar inda aka wayi gari da murabus din shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar
A halin yanzu dai shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas Simi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Gwamnan ya isa fadar shugaban kasa da misalin karfe 5:35 na yamma. sannan ya wuce kai tsaye zuwa ofishin shugaban kasa.
KARANTA WANNAN: ‘Yan Sanda Sun Kame Wani Sojan Karya a Jihar Nasarawa
Ba kamar na karshe da ya zo fadar gwamnatin tarayya tare da tawagar magoya bayansa a yayin ganawar zaman lafiya da ubangidansa na siyasa kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da shugaban kasa, gwamnan ya zo shi kadai a yau.
Ko da yake ba a bayyana ajandar ziyarar tasa ba a lokacin gabatar da wannan rahoto, amma watakila bai rasa nasaba da rikicin siyasar da ya barke tsakanin gwamnan da ministan babban birnin tarayya, game da mulkin jam’iyyar PDP a jihar Ribas.
A wani labarin kuma, Kotun Koli Ta Tabbatar Da Nasarar Zaben Gwamnan Akwa Ibom
Kotun koli ta yi watsi da kararraki uku da jam’iyyun APC, YPC da NNPP da ‘yan takararsu suka yi kan gwamnan jihar Akwa Ibom
Jam’iyyun dai sun bukaci kotun kolin da ta tsige gwamnan jihar, bisa zargin yin takardar shaidar jabu
Wannan hukunci dai bai yiwa masu kara dadi ba wanda ya zama wajibi su rungumi kaddara
A ranar Alhamis ne kotun koli ta yi watsi da kararraki uku da jam’iyyun APC, YPC da NNPP da ‘yan takararsu suka yi kan gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno.
Hakan ya biyo bayan lauyoyin masu ruwa da tsaki a lamarin sun yanke shawarar janye karar.