- Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana shirinta na dakile duk wani hargitsin da ka iya tasowa biyo bayan hukuncin da kotun koli za ta yanke
- Wannan dai na zuwa ne bayan gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar, NNPP, ya shigar da kara kan korar da kotun daukaka kara ta yi masa
- Rundunar ta aiwatar da matakan tsaro domin baiwa mazauna jihar damar ci gaba da sana’o’insu na halal ba tare da wata barazana ba
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana shirinta na dakile duk wani hargitsin da ka iya tasowa biyo bayan hukuncin da kotun koli za ta yanke na gobe kan karar da gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar, NNPP, ya shigar kan korar da kotun daukaka kara ta yi masa.
Rundunar ‘yan sandan ta baiwa mazauna jihar tabbacin tsaron lafiyarsu kafin da kuma lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu, Gwamnan Ribas Fubara Sun Shiga Ganawar Sirri a Villa
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Hussaini Gumel ne ya bayar da wannan tabbacin yayin wata tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Alhamis.
Gumel ya bayyana cewa rundunar ta aiwatar da matakan tsaro domin baiwa mazauna jijar damar ci gaba da sana’o’insu na halal ba tare da wata barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.
Ya ce, “Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro a duk wuraren da ake tashe-tashen hankula, da suka hada da ofisoshin jam’iyyun siyasa, gidan gwamnatin jihar, hedikwatar INEC, bankuna da wuraren kasuwanci, masallatai, coci-coci, wuraren shakatawa da wuraren ajiye motoci kafin, lokacin da kuma bayan hukuncin.
“Ina ba da tabbacin kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna jihar masu bin doka da oda da su gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji Kwamishinan.
Ya ce jami’an tsaron da ke dauke da makamai za su kasance a duk wuraren da aka san su don tabbatar da cewa sun fara aikin sa ido da samar da tsaro a lokacin da kotun koli za ta yanke hukunci da kuma bayan yanke hukunci.
A wani labarin kuma,’Yan Sanda Sun Kame Wani Sojan Karya a Jihar Nasarawa
Rundunar ‘yan sandan Nasarawa, ta bayyana cewa jami’ansu sun kama wani fitaccen dan fashi da makami da wani sojan bogi
Ku tabbata ba kuyi kasa a gwiwa ba wajen yakar masu aikata laifuka a jihar
Kamen ya biyo bayan samun sahihan bayanai da jami’an rundunar ‘yan sandan suka yi wajen awon Gaba da masu laifin
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, a ranar Alhamis, ta bayyana cewa jami’ansu sun kama wani fitaccen dan fashi da makami da wani sojan jabu sanye da rigar sojoji.
DSP Ramhan Nansel, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, CP Shehu Nadada.