- Gwamnan Oyo, Seyi Makinde da kuma korarrun shugabannin kananan hukumomin jihar da alama sun warware rashin fahimtar juna da suka yi
- Wannan ci gaban ya samo asali ne sakamakon tsoma bakin ministan lantarki, yayin ziyarar aiki da ya kai ofishin gwamna
- A baya dai Gwamnan ya kori shugabannin kananan hukumomin bayan hawan sa mulki
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da kuma korarrun shugabannin kananan hukumomin jihar a ranar Litinin, da alama sun warware rashin fahimtar juna da suka yi, kamar yadda aka ce gwamnan ya yi alkawarin biyan su alawus-alawus.
Wannan ci gaban ya samo asali ne sakamakon tsoma bakin ministan wutar lantarki, Bayo Adelabu, yayin ziyarar aiki da ya kai ofishin gwamna.
KARANTA WANNAN: Wasu Mutane ‘Yan Kalilan Ne Suka Wawure Arzikin Najeriya Ta Hanyar Tallafi’ – Tinubu
A cikin tawagar ministan har da tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi da aka kora, Ayodeji Abass-Aleshinloye, wanda gwamnan ya kora bayan hawansa mulki.
Wata majiya mai tushe daga gwamnatin ta ce, “A yau an samu zaman lafiya tsakanin gwamnatin jihar da kuma korarrun mambobin kungiyar kananan hukumomin Najeriya kamar yadda gwamnan ya yi alkawarin sakin asusansu nan take.
“Ministan, Adelabu, ya shiga tsakani a rikicin, inda ya yi kira ga gwamnati da wakilin tsoffin ALGON da Aleshinloye ya wakilta da su rungumi zaman lafiya.
“Ministan ya yi wannan katsalandan ne a ranar Litinin, a sakatariyar jihar yayin ziyarar aiki da ya kai wa gwamnan jihar, Makinde.”
Majiyar ta kara da cewa “Adelabu ya shiga cikin lamarin ne a wata ganawar sirri da gwamnan da Aleshinloye, inda gwamnan ya yi alkawarin biyan bashin kudaden su nan take.
“Kafin su shiga ganawar sirri, an hangi wasu daga cikin manyan mataimakan gwamnan da wasu daga cikin ayarin ministan ciki har da Olayemi Gbenga, Segun Olalere yayin da suke tattaunawa yayin da wasu suka yi musayar kalamai.
“A ci gaban da ya biyo baya, daga baya Makinde ya ci gaba da musabaha da Aleshinloye a takaice bayan kammala taron cikin lumana.”
A wani labarin kuma, Uzodinma: Tinubu Ya Gana Da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo
Shugaban kasa Tinubu ya gana da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
Duk da ziyarar Tinubu, Obasanjo ya goyi bayan jam’iyyar Labour Party LP
A baya dai Tinubu da Obasanjo sun sha fama da tsamin dangantaka
A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya rungumi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo tare da yin musabaha.
Mutanen biyu sun gana ne a yayin rantsar da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo a Owerri a karo na biyu.