- Shugaban kasa Bola Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro a Abuja
- Wannan dai na zuwa ne kan karuwar matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a fadin kasar
- Taron na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Ministan babban birnin tarayya ya kira nasa taron tantance harkokin tsaron
Shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Talata ya gana da hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro a fadar gwamnati da ke Abuja.
Wannan dai na zuwa ne kan karuwar matsalar rashin tsaro da ake fama da ita.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Na Ci Gaba Da Jajircewa Kan Shugabancin Tinubu – Buhari
Sannan hakan na zuwa ne a daidai lokacin da aka sake samun sabbin tashe tashen hankula a wasu sassan kasar nan, musamman a babban birnin tarayya Abuja, inda masu garkuwa da mutane suka tafka munanan ayyuka a cikin ‘yan kwanakin nan.
A wajen taron akwai babban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Christopher Musa; Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja; Babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogala; Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshal Hassan Abubakar; Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da shugaban wasu jami’an tsaro.
Duk da cewa babu wani bayani a hukumance game da taron har yanzu, ana kyautata zaton cewa shugaba Tinubu da hafsoshin tsaronsa za su yi nazari a kan al’amuran tsaro na baya-bayan nan a sassan kasar nan.
Sannan za su ba da shawarwarin yadda za a shawo kan ‘yan ta’addan masu aikata laifuka da suka hada da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi.
Taron kuma na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da Ministan babban birnin tarayya, Cif Nyesom Wike, ya kira nasa taron tantance harkokin tsaro, kan ta’addancin da masu garkuwa da mutane suka yi wa mazauna kujerar mulki, inda suka yi ta kisan gilla da kuma neman a biya su makudan kudade daga hannunsu wadanda abin ya shafa.
A wani labarin kuma, Wata Mummunar Gobara Ta Lakume Dukiya Ta Miliyoyin Naira A Jihar Kwara
Wata mummunar gobara da ta tashi a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta yi asarar dukiya ta miliyoyin naira
Mummunar gobarar ta lakume wa sama da mutane 120 matsugunansu
Ana zargin wani mutum da ba a san ko wanene ba ya cinna wuta, tun da farko inda ta bazu
Wata mummunar gobara da ta tashi a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta yi asarar dukiya ta miliyoyin naira a ranar Litinin, inda sama da mutane 120 suka rasa matsugunansu.
Hatsarin farko ya afku ne da misalin karfe 11:08 na safe, kamar yadda kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Hassan Adekunle, ya bayyana a wata sanarwa a Ilorin ranar Litinin.