Premier ta Sanya Ranar da za a saurari tuhume-tuhume 115 da ake yi wa Man City
Shugaban Premier League Richard Masters ya tabbatar da cewa “an sanya ranar” don sauraron tuhume-tuhumen da ake wa Manchester City kan karya dokar kashe kudade.
A watan Fabrairun da ya gabata an tuhumi City da keta dokokin kuɗi 115, biyo bayan binciken shekara hudu aka gudanar.
A cikin wata Sanarwa da Premier ta fitar ta ce “sun mika wasu laifuka da ake zargin Man City da aikatawa daban-daban tun daga kakar wasa ta 2009/2010 ga wata hukuma mai zaman kanta.
City sun dage cewa ba su da laifi kuma suna da’awar cewa suna da “cikakkiyar shaidun da ke nuna rashin laifin su, kuma za su iya l wanke su daga dukkanin zarge-zargen da ake musu.
KARAN WANNAN LABARIN:“Ƴan Matan Mijina 87 ne a lokacin da na haɗu da shi” Ƴar Gwagwarmaya
An tambayi Richard game da lamarin, a lokacin da bayyana a gaban wani Kwamiti, da kuma wata kafar Watsa Labarai da shirin Wasanni.
Akwai ranar da aka Sanya don sauraren waɗannan tuhume-tuhumen; Amma ku yi haƙuri, ba zan iya gaya muku lokacin da aka yake ba amma tabbas nan kusa ne.
“Ba zan iya ba da wani cikakken bayani kan Man City da ya wuce na ce an sanya kwanan watan sauraren ƙarar ba;
Ba zan iya gaya muku lokacin da wannan ranar za ta kasance ba, ”in ji shi.
A wani labarin kuma:TSARO: Gwamnatin Najeriya za ta ƙulla Alaƙa da Faransa domin magance tsaro
TSARO: Gwamnatin Najeriya za ta ƙulla Alaƙa da Faransa domin magance tsaro
Gwamnatin Najeriya ta kara zurfafa alaka da ƙasar Faransa kan rashin tsaron da ke addabar kasar.
Ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar a ranar Talata ne ya bayyana shirin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na karfafa alakarta da kasar Faransa domin magance matsalar rashin tsaro.
Ya ce dangantaka da Faransa na da matukar muhimmanci wajen magance matsalar ‘yan Ta’adda, da sauran laifuka a kasar.
Ya bayyana haka ne a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin ‘yan Majalisar Faransa da kuma tawagar Jami’an hukumar tsaron kasar ƙarƙashin Jagorancin Gassilloud Thomas a Abuja.