- Yanzu haka dai an saki tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye daga gidan gyaran hali na Kuje
- Kafin sakin sa wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin tsare tsohon ministan a gidan kurkukun Kuje kan kwangilar dala biliyan 6
- Aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, wanda aka fara shi a shekarar 2003, ya sha fama da tashe-tashen hankula na shari’a da zargin cin hanci da rashawa
Yanzu haka dai an saki tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye daga gidan gyaran hali na Kuje bayan da ya cika sharadin belinsa.
Wakilinmu ya samu labarin cewa an saki Agunloye ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: CBN Ya Sanya Ranar da Zai Gudanar Da Taron MPC
Kakakin Hukumar kula da gidan gyaran hali da tarbiyya na babban birnin tarayya Abuja Adamu Duza, ya tabbatar wa wakilinmu hakan.
Duza ya ce, “An sako Agunloye daga gidan yari bayan cika sharuddan belinsa. An sake shi a yammacin yau da misalin karfe 5:30 na yamma.”
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Agunloye a gidan kurkukun Kuje kan kwangilar samar da wutar lantarki ta Mambilla ta dala biliyan 6.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da Agunloye a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ya ki amsa tuhumar da ake masa.
Sai dai alkalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare Tsohon ministan a gidan yari na Kuje har zuwa lokacin da za a bayar da belinsa.
Idan dai za a iya tunawa, EFCC ta bayyana neman Agunloye ne a kan wani shirin samar da wutar lantarki na dala biliyan 6 wanda ya hada da aikin samar da wutar lantarki ta Mambilla.
EFCC ta yi zargin cewa Agunloye, wanda ya rike mukamin minista a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2003, a karkashin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayar da kwangilar gina tashar samar da wutar lantarki ta Mambilla mai karfin MW 3,960 a kan gine-gine, gudanar da aiki, da canja wuri.
Hukumar ta shaida wa kotun cewa kwangilar da aka bayar ga Kamfanin Sunrise Power and Transmission Company Limited, an yi ta ne ba tare da wani tanadi na kasafin kudi ba, ko amincewa, ko tallafin kudi.
Hakazalika ana zargin Agunloye da laifin karbar cin hanci har naira miliyan 3.6 daga kamfanin da ya ba kwangilar.
Sai dai wanda ake tuhumar wanda kuma ya taba rike mukamin karamin ministan tsaro, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a lokacin da aka kai shi gidan yari, duk da cewa kotu ta tsare shi a gidan yari na Kuje har sai an yanke hukunci kan neman belinsa.
Aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, wanda aka fara shi a shekarar 2003, ya sha fama da tashe-tashen hankula na shari’a da zargin cin hanci da rashawa.
A wani labarin kuma, Mafarauta Sun Ceto Wata Bazawara da ‘Ya’yanta a Jihar Kebbi
Mafarauta a jihar Kebbi sun kubutar da wata mata da ‘ya’yanta biyu daga daji
Tunda farko an kai matar da ‘ya’yanta cikin dajin ne bayan an hallaka mijinta saboda ta ki aurar mamban kungiyar ‘yan fashin
Kungiyar mafarautan da kuma jami’an tsaron dazuzzukan suna aiki tare da sauran jami’an tsaro domin magance ‘yan fashi a jihar
Mafarauta a jihar Kebbi sun kubutar da wata mata da ‘ya’yanta biyu daga daji bayan wasu ‘yan bindiga sun hallaka mijinta.
An kai matar da ‘ya’yanta cikin daji bayan an hallaka mijinta saboda ta ki aurar mamban kungiyar ‘yan fashin.