- Mai magana da yawun gwamnan Osun, Olawale Rasheed, ya ce ba za a janye shawarar da aka yanke kan batutuwan da suka shafi sarauta a jihar ba
- Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta ba da umarnin sake zabar sabbin kujerun sarakunan bayan ta soke tsarin da ya samar da su
- Gwamnati ta tsaya tsayin daka kan matakin da aka dauka kuma ta na kira ga jama’a da su yi watsi ga duk wani rahoto da ya saba wa doka
Mai magana da yawun gwamnan jihar Osun, Olawale Rasheed, ya ce ba za a janye shawarar da aka yanke kan batutuwan da suka shafi sarauta kamar yadda yake kunshe a cikin farar takarda da gwamnatin jihar ta fitar a ranar Alhamis ba.
Gwamnatin jihar Osun ta ba da umarnin sake zabar sabbin kujerun sarakunan Aree na Iree da Owa na Igbajo, bayan da ta soke tsarin da ya samar da su.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: An Saki Tsohon Ministan Lantarki Daga Gidan Yari
Gwamnatin ta kuma bayyana kujerar Akinrun na Ikirun, Oba Olalekan Akadiri a matsayin wanda babu kowa, tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su jira a yanke hukunci kan kujerar da ke gaban kotun daukaka kara.
Rasheed, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Osogbo, babban birnin jihar a ranar Juma’a, ya ce bayanin ya zama dole ne biyo bayan labaran karya da ke cewa gwamnati za ta koma kan matakin da ke kunshe a cikin wata farar takarda kan batun sarautar.
Kakakin ya ce gwamnan, Ademola Adeleke ya yabawa mutane da masu ruwa da tsaki na garuruwan da abin ya shafa bisa kyakkyawar tarbar da suka yi da farar takardar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “An jawo hankalin Sashen Yada Labarai na Gwamnan Jihar Osun kan labaran karya game da yadda gwamnati za ta koma kan matakin da ke kunshe a cikin wata farar takarda kan batun sarauta da aka fitar jiya.
“Wanda ya yi karyar ya tabbatar da gaskiyar ikirarin da mai magana da yawun gwamnan jihar Osun ya yi.
“Babu kanshin gaskiya a cikin rahoton kuma ya kamata a dauke shi a matsayin hannun masu cin gajiyar haramcin da gwamnatin da ta shude ta yi.
“Muna so mu nanata cewa gwamnati ta tsaya tsayin daka kan matakin da aka dauka na farar takarda kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani rahoto da ya saba wa doka.
“A kowane lokaci ban yi ko fitar da wata sanarwa ba kamar yadda aka amince da ni. Jama’a su yi watsi da shi gaba daya.
“Mai girma gwamna ya yaba da yadda aka yi masa kyakkyawar tarbar sakamakon da aka yi bisa tsarin da ya dace, bin doka da oda da al’adar jama’a.”
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: CBN Ya Sanya Ranar da Zai Gudanar Da Taron MPC
Kwamitin manufofin kudi na babban bankin Najeriya zai gudanar da taron manufofinsa na farko na wannan shekara
Taron wanda zai kasance karo na farko a karkashin jagorancin Gwamna Yemi Cardoso an shirya zai kasance daya daga cikin taruka shida a bana
A shekarar da ta gabata MPC ta gana a watan Yuli, karkashin tsohon gwamnan da aka dakatar, Godwin Emefiele
Kwamitin manufofin kudi na babban bankin Najeriya zai gudanar da taron manufofinsa na farko na wannan shekara a ranakun 26 da 27 ga watan Fabrairu.
Wannan bisa ga kalandar taron MPC ne da aka wallafa a gidan yanar gizon babban bankin.