“Yanzu haka Hanyoyi 320 ne muke kan gyarawa” – Umahi
Ministan ayyuka Sanata Dave Umahi ya bayyana cewa a yanzu haka Ma’aikatar tana aikin samar da hanyoyi 320 a faɗin ƙasar nan domin kawo tallafi ga al’umma ta fuskoki daban daban.
Da yake magana a wata ganawa da yayi da Ministan Tsaro Mohammed Badaru Abubakar da babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, Umahi ya ce, inganta hanyoyin zai samar da ababen more rayuwa, kuma zai inganta harkar noma da harkokin kasuwanci a faɗin ƙasar nan.
Yayin da yake bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwa wajen inganta harkokin tsaro a cikin kasar Najeriya, ta hanyar kawo sauyi ga ayyukan samar da ababen more rayuwa a titunan kasar, ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shirya tsaf don inganta rayuwar ‘yan Najeriya ta hanyar samar da ingantattun hanyoyin sufuri.
KARANTA NAN:Majalisar dattawa za ta gayyaci Wike kan matsalar ƴan bindiga a Abuja – Ireti
Da yake Jawabi a madadin tawagar da suka kai ziyarar, Babban hafsan sojin kasar ya bayyana cewa, mahimmancin taron shi ne tattauna batutuwan da suka shafi goyon bayan ikon kasa ga ayyukan soji tare da mai da hankali kan rawar da ake takawa wajen inganta ababen more rayuwa domin inganta ayyukan Sojiji a faɗin kasar.
Mun tattauna sosai, kuma mun yi farin ciki da cewa Honarabul Ministan Ayyuka zai yi amfani da wasu muhimman shawarwarin da muka bayar game da bukatar mayar da hankali kan gyara wasu muhimman hanyoyin sufuri da za su yi tasiri ga ayyukan soja a faɗin kasar nan. Don haka Ministan Ayyuka ya yi wasu alkawura, kuma muna sa ran ganin aiwatarwar ’yan kwangila da sauran wakilai, sun mayar da hankali a wannan fanni kuma sojoji za su tallafa musu su ci gaba da hakan. Gabaɗaya inganta tsaro ita ce manufarmu kuma za mu ci gaba da yin ƙoƙari domin tabbatuwar hakan.
A wani labarin kuma:Rashin aiwatar da Manufofi yadda ya dace , ke da alhakin Wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke sha – Sanata Moro
Rashin aiwatar da Manufofin yadda ya dace , ke da alhakin Wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke sha – Sanata Moro
Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, kuma Sanata mai wakiltar mazabar Benuwe ta Kudu Abba Moro ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala a halin yanzu saboda rashin aiwatar da manufofin Gwamnati da aka bijiro domin inganta rayuwarsu.
Moro wanda ya bayyana hakan a Makurdi ta Jihar Binuwai yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a karshen mako, ya yi tir da yadda matsalolin da ke addabar kasar nan, ya nuna cewa Majalisar dattawa za ta yi duk mai yiwuwa don dakatar da wannan lamarin.