- Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birniwa a jihar Jigawa, Alhaji Talba Diginsa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC
- ‘Yan majalisar zartarwa na jam’iyyar PDP tare da mambobi 360 sun fice daga jam’iyyar saboda rashin shugabanci na gari a jihar
- APC ta yi alkawarin yin aiki da sabbin mambobin jam’iyyar domin samun nasarar jam’iyyar
Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birniwa a jihar Jigawa, Alhaji Talba Diginsa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da magoya bayansa.
Diginsa ya ce ‘yan majalisar zartarwa na jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar tare da mambobi 360 sun fice daga jam’iyyar saboda rashin mayar da hankali da kuma rashin shugabanci na gari a jihar.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ba Shi Da Shirin Sauyawa Babban Birnin Najeriya Matsuguni – Fadar Shugaban Kasa
Ya kara da cewa, “Mun yanke shawarar barin PDP ne duk da mukaman da muke da shi a jam’iyyar saboda kyakkyawan jagoranci da jajircewar Gwamnan Jihar Jigawa na yanzu, Mallam Namadi, a cikin watanni shida kacal da ya kwashe yana mulki.
“Muna da tabbacin gwamna Mallam Umar Namadi zai samu nasarar gudanar da mulkin jihar ta hanyar duba ajandarsa mai maki 12.”
Da yake jawabi bayan karbar ‘ya’yan PDP da suka sauya sheka a Kwanar Dole, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Aminu Sani Gumel ya ce jam’iyyar APC a shirye take ta karbi kowa don ci gaban jam’iyyar.
Gumel ya yi alkawarin yin aiki da sabbin mambobin jam’iyyar domin samun nasarar jam’iyyar.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Daga karshe Dai Gwamnan Ondo Aiyedatiwa Ya Nada Mataimakinsa
Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya nada Cif Olayide Owolabi Adelami a matsayin mataimakin gwamnan
Wannan na Zuwa ne ‘yan sa’oi kadan bayan da Gwamnan ya rusa majalisar zartarwa ta jihar
Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar bayan rasuwar Rotimi Akeredolu
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya nada Cif Olayide Owolabi Adelami a matsayin mataimakin gwamna a hukumance.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tuna cewa Aiyedatiwa ya zama gwamnan jihar Ondo bayan rasuwar Rotimi Akeredolu.