- Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayar da tabbacin a shirye ta ke ta samar da tsaro a zaben da za a sake gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu
- “Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe
- “Duk mutumin da ba shi da katin zabe na dindindin ba zai shiga zaben da za a sake yi ba”
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da tabbacin a shirye ta ke ta samar da tsaro a zaben da za a sake gudanarwa a ranar 3 ga watan Fabrairu a mazabu uku na kananan hukumomi shida na jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Hussaini Gumel, ne ya bayar da wannan tabbacin ranar Laraba a Kano a lokacin da yake zantawa da manema labarai gabanin zaben.
KARANTA WANNAN: Gwamna Bello Ya Mika Sandar Mulki Ga Basaraken Gargajiyar Ohimeghe Igu Na Koton-Karfe
Gumel ya ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a jihar na kokarin ganin an gudanar da zabe ba tare da rikici ba.
Ya ce an riga an samar da ingantaccen tsarin aiki kan yadda za a samar da tsaro a kowacce rumfunan zabe domin aiwatarwa.
“Mun tattara isassun jami’an tsaro da za su samar da tsaro kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.
“Ina ba da tabbacin kashi 100 cikin 100 ga duk mazauna mazabun masu bin doka da oda, cewa za su iya tafiya cikin walwala don gudanar da aikinsu a ranar 3 ga watan Fabrairu ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” inji shi.
Ya ce matakan tsaro da aka sanya za su baiwa wadanda suka cancanci kada kuri’a damar shiga dukkan harkokin zabe.
“Mun sanya matakan tsaro daban-daban domin baiwa mazauna yankin damar shiga zaben shugabannin da suke so ba tare da barazana ga rayuka da dukiyoyi ba,” in ji shi.
Kwamishinan ‘yan sandan ya shawarci shugabannin jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su ja hankalin magoya bayansu da su guji duk wani nau’in tashin hankali da ‘yan daba kafin zabe da lokacin da kuma bayan zabe.
“Ba za mu amince da duk wani aiki da zai iya kawo rudani kafin, lokacin da kuma bayan zaben cike gurbi ba, duk wani mutum ko kungiyar da aka samu da kin bin umarni za a kama su a gurfanar da su a gaban kuliya,” inji shi.
Tun da farko, Kwamishinan Zabe na jihar (REC), Ambasada Abdu Zango, ya ce an kammala shirye-shiryen gudanar da zabukan da za a sake gudanarwa a mazabu uku na Jihar da abin ya shafa.
Ya lissafa mazabun kamar haka: Kunchi/Tsanyawa, Kura/Garun Malam da Rimin Gado/Tofa.
“Mun shirya tsaf domin sake gudanar da zabukan, tare da horar da jami’an zabe a shirye don gudanar da sahihin zabe a kananan hukumomi shida.
“Zamu gudanar da zabe a rumfunan zabe 66 a fadin kananan hukumomi shida. Duk mutumin da ba shi da katin zabe na dindindin ba zai shiga zaben da za a sake yi ba,” inji shi.
Ya ce za a yi amfani da na’urar BVAS a yayin sake gudanar da zabukan domin tabbatar da sahihin zabe da kuma inganci.
Zango ya bayyana kwarin gwiwar cewa za a sake yin zaben cikin nasara.
“Mun shirya da kuma baiwa jami’anmu kayan aikin da za su iya gudanar da zabuka cikin ‘yanci, gaskiya da adalci,” inji shi.
A wani labarin kuma, Hawaye Sun Kwaranya: Muhammad Umar Ngelzarma Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Sa
Alhaji Umaru Ngelzarma (A.U.N) Ya kasance dan kasuwa mai gudanar da harkokin kasuwanci a masana’antar mai da iskar gas kuma sananne a duk fadin Najeriya.
Sannan Yana Daya daga cikin tsofaffin dillalan albarkatun man fetur a cikin al’umma baki daya.