- Gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya mika sandar mulki ga sarkin masarautar Koton-Karfe na 27
- Gwamnan jihar ya hori Sarkin da ya yi amfani da ofishinsa wajen kare al’ummarsa da kuma al’ummar masarautar da yake mulka
- A ranar 26 ne dai Gwamnan Jihar ya tsige basaraken Gargajiya na Ohimeghe na Koton-Karfe, Alh. Abdulrazak Isa Koto
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya mika sandar mulki ga sarkin masarautar Koton-Karfe na 27 Ohimege Igu, HRM. Saidu Akawu Salihu.
Sabon Sarkin wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Gargajiya ta Lokoja/Kogi/Koton-Karfe ya karbi bakuncin ma’aikatan sa na Zinare a fadar sa ta Koton-Karfe cikin murna da annashuwa.
KARANTA WANNAN: Hawaye Sun Kwaranya: Muhammad Umar Ngelzarma Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifin Sa
Idan za a iya tunawa a ranar 26 ne dai Gwamnan Jihar Yahaya Bello ya tsige Ohimeghe na Koton-Karfe, Alh. Abdulrazak Isa Koto.
Yayin da yake gabatar da sandar mulki ga sarkin gargajiya, Gwamna Yahaya Bello ya hori Sarkin da ya yi amfani da ofishinsa wajen kare al’ummarsa da mazauna da kuma al’ummar masarautar Igu.
Yahaya Bello ya yabawa al’ummar garin Koton-Karfe bisa tsayawar gaskiya da kuma ba da damar gudanar da zaben Ohimeghe na Koton-Karfe.
A nasa martanin, Basaraken Gargajiyar Ohimege Igu na Koton-Karfe, ya gode wa Gwamna Bello bisa tsayawar gaskiya da samar da hanyar yin adalci.
Ya ce, “Na gode wa Allah da na ga wannan rana, ina kuma gode wa gwamnatin Jihar Kogi a karkashin jagorancin mai girma, Alhaji Yahaya Bello bisa jajircewar da ta yi wajen gyara wani babban kuskure.
“Ta wannan mataki na musamman ya ceci cibiyarmu da ta dade a gargajiyance daga ba’a ga jama’a tare da hana zubar da hukuncin sarakunanmu.”
Ya yi alkawarin yin hidima cikin tawali’u, gaskiya, sadaukarwa da kuma kiyaye al’adu da kimar masarautar Igu.
Sannan ta kara da cewa “Zan zama kunnuwan sauraro, mai ba da shawara mai karfi kuma mai gina gada”.
An haifi Dr. Saidu Akawu Salihu a ranar 11 ga watan Maris din shekarar 1964 kuma ya kasance iyalan marigayi Chief Salihu Umar Danmadaki da marigayiya Hajiya Aishetu Salihu na Odaki- Koton-Karfe a karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi.
Mai Martaba Sarki ya fara karatun firamare a Kogi L.S.B Koton-Karfe tsakanin shekarun 1970-1976.
A shekarar 2012, HRM Salihu ya tsaya takara a matsayin Ohimege, kuma Sarakunan sun amince da shi amma da aka tsige Ohimege ya samu goyon bayan gwamnatin da ta gabata, aka nada shi a ranar 12 ga watan Oktobar shekarar 2012.
A wani labarin kuma, Shugaban PDP da Wasu Sun Koma APC a Jigawa
Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birniwa a jihar Jigawa, Alhaji Talba Diginsa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC
‘Yan majalisar zartarwa na jam’iyyar PDP tare da mambobi 360 sun fice daga jam’iyyar saboda rashin shugabanci na gari a jihar
APC ta yi alkawarin yin aiki da sabbin mambobin jam’iyyar domin samun nasarar jam’iyyar
Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birniwa a jihar Jigawa, Alhaji Talba Diginsa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da magoya bayansa.
Diginsa ya ce ‘yan majalisar zartarwa na jam’iyyar PDP a Karamar Hukumar tare da mambobi 360 sun fice daga jam’iyyar saboda rashin mayar da hankali da kuma rashin shugabanci na gari a jihar.