- Wata Kotun Laifukan Jima’i da Laifukan Cikin Gida da ke Ikeja ta yanke wa wani Bishop a Legas, Oluwafeyiropo Daniels, hukuncin daurin rai da rai
- Hakan ya biyo bayan laifin yin lalata da mataimakiyar sa ‘yar shekara 23
- Alkalin kotun ya ba da umarnin cewa malamin ya ci gaba da zama a gidan kurkukun Kirikiri
Wata Kotun Laifukan Jima’i da Laifukan Cikin Gida da ke Ikeja ta yanke wa wani Bishop a Legas, Oluwafeyiropo Daniels, hukuncin daurin rai da rai kan laifin yi wa mataimakiyar sa ‘yar shekara 23 fyade (wanda aka sakaya sunanta).
Mai shari’a Rahman Oshodi ya kuma yankewa Daniels, Bishop na cocin I Reign Christian Ministry dake Legas, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin yin lalata da wata mambar cocin ‘yar shekara 19.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Jurgen Klopp Zai Sauka Daga Matsayin Kocin Liverpool
Alkalin kotun ya ba da umarnin cewa malamin ya ci gaba da zama a gidan kurkukun Kirikiri da ke Legas.
Mai shari’a Oshodi ya bayyana cewa, masu gabatar da kara sun tabbatar da sinadaran laifukan biyu.
A cewarsa, Daniels maƙaryaci ne kuma ba ya kula da gaskiya.
Sai dai alkali ya sallame shi kuma ya wanke shi bisa wasu zarge-zarge biyu da ake tuhumarsa da su, wato fyade ga wata mambar cocin (Wadda aka sakaya sunanta).
Oshodi ya ce akwai wani bangare na yarda daga dan cocin.
Alkalin ya kuma sallame tare da wanke Daniels a kan tuhume-tuhume hudu da ake zarginsa da yunkurin yi wa wata mambar majami’ar fyade.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa, Daniels ya fuskanci tuhuma guda hudu da aka yi wa kwaskwarima da suka hada da fyade, yunkurin fyade da kuma cin zarafi.
Fyade ya ci karo da sashe na 260 (2) na dokokin laifuka na jihar Legas shekarar 2015.
A wani labarin kuma,Yanzu-Yanzu: An Kwantar da Sarkin Ingila Charles Asibiti
Fadar Buckingham ta bayyana cewa an kwantar da Sarkin Ingila Charles III a asibiti
A farkon makon da ya gabata ne fadar ta sanar da cewa za a dage taron jama’a na Sarki Charles na III
Fadar tace anyi hakan ne don bai wa Sarkin damar jinya na wani dan kankanin lokaci
Fadar Buckingham ta bayyana cewa an kwantar da Sarkin Ingila Charles III a asibiti domin yi masa tiyatar mafitsara a safiyar Juma’a.
LEADERSHIP ta rawaito cewa a farkon makon da ya gabata ne fadar ta sanar da cewa za a dage taron jama’a na Sarki Charles na III na wani dan kankanin lokaci domin ya je asibiti domin jinyar cutar mafitsara.