Najeriya Na Buƙatar Sirinji Biliyan 12 Don kula da Masu Jinya a Asibitocin kasar nan
Ana bukatar akalla Sirinji Biliyan 12 domin biyan bukatun ‘yan Najeriya da ake jinya a faɗin Asibitocin kasar.
Wannan ya fito ne a cewar Manajan Daraktan Kamfanin Afrimedical Manufacturing & Supplies Ltd wato Akin Oyediran.
Da yake magana a wani taro da masu ruwa da tsaki na masana’antu ya ce, Kamfanonin da ke sarrafa Sirinji a kasar nan suna samar da sirinji kimanin biliyan uku, inda ya ƙara da cewa idan aka yi kyakkyawan tsari to Najeriya na da kyakkyawar dama ta zama mai fitar da Sirinji da allura zuwa ƙasashen ketare.
Ya ce wasu daga cikin Sirinjin da ake shigowa da su kasar a halin yanzu ba su da inganci, amma waɗanda ake kerawa a kasar sun kasance mafi inganci kuma sun samu amincewar hukumar lafiya ta duniya (WHO) da Hukumar NAFDAC da sauran hukumomin lafiya da abin ya shafa.
KARANTA NAN:Da Dumi-Dumi: An Yanke Wa Bishop Hukuncin Daurin Rai da Rai Bisa Wasu Tuhume-Tuhume
A nasu ɓangaren, karamin ministan lafiya Dr Tunji Alausa da Ministan kasuwanci da zuba jari na masana’antu Doris Nkiruka Uzoka Anite sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarinn bunƙasa masana’antar allura da Sirinji a ƙasar nan.
Alausa ya ce Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya umarce su da su duba hanyoyin da za a bi domin rage tsadar magunguna da allurai a ƙasar nan.
Ya ce an samar da hanyoyin da suka dace don magance kalubalen, inda ya ce hanyoyin za su sanya allura da masana’antar sarrafa Sirinji a kan turbar dorewa, inda za ta fara samar da ayyukan yi mai kyau ga ‘yan kasa da samar da allurai da Sirinji masu inganci wadanda za su iya samar da ingantattun allurai da Sirinji. Ba zai zama cutarwa ga ‘yan ƙasa ba yayin da suke ziyartar asibitoci ko wuraren kula da lafiya don neman kulawa ba” inji shi.
Uzoka Anite ya ce daya daga cikin kyawawan manufofin da aka samar don kawar da tarnaki ga masana’antu a cikin gida Najeriya shine samar da wani tsarin haɗaka wanda ya kunshi manufofin da suka shafi na’urorin likitanci.
Ta ce nan ba da dadewa ba za a ƙaddamar da shirin haɗakar na baya bayan nan da zarar Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shi.
Wannan wata manufa ce da za ta zama tsanin canjin salonbaiki ga na’urorin Masana’antun likitanci, ”in ji ta.
Shugaban kungiyar masu kera na’urorin likitanci na Najeriya Dr. Lanre Shittu ya bayyana taron a matsayin mai tarihi, ya ƙara da cewa hanyoyin da ake bi na amfani da su za su taimaka wajen dakile matsalar da kamfanin na’urorin likitanci ke fuskanta na barin kasar.