Wata Kungiya Yan Kasuwa a Jihar Bauchi dake rajin taimaka wa Marayu mai suna Laushi Wunti Market Al’ansar Trust Fund for Orphans Multi-purpose Cooperative Society tabtaimaka wa marayu sama da dari da talatin da kayan azumi.
Kayayyakin sun hada da buhun shinkafa da na gero da na dawa gami da atamfofi da dai sauransu.
Da yake jawabi yayin rabon kayayyakin, Shugaban Kwamitin Rabon Kayayyakin Wada Baba Magaji ya ce an taimaka wa marayun ne don rage musu radadin rayuwa a musamman a watan na Ramadan.
Wada Baba Magaji ya bayyana cewa duk shekara Kwamitin na raba irin wannan kayayyaki ta hanyar kutare da kungiyar ke hadawa daga hannayen mambobin ta ko wane mako.
Ya kuma ce ƙungiyar na kara kokarin sake nemo wata hanya da za ta rika taimaka wa marasa karfi a tsakanin al’umma musamman a lokacin Azumi ko Sallah.
Daga bisani ya jaddada bukatar dake da akwai na ga Gwamnati da ma masu hannu da shuni tsakanin al’umma na taimakawa wajen kyautata rayuwar marayu.
Wasu daga marayun da suka ci gajiyar tallafin jayan azumin Khadijah Adamu da Kuma Salisu Adamu sun bayyana farin cikin su matuƙa tare da bayyana alwashin su na amfani da dukiyar ta hanyar da ta dace.