Ta tabbata cewar shahararren ɗan wasannan wato Christiano Ronaldo da yake taka ledarsa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juvebtus dake ƙasar Italiya ya warke daga jinyar cutar nan ta Coronavirus. Ya warke ne biyo bayan gwaji da aka yimasa a wanann yammaci na Juma’a.
Ronaldo dai ya kwashe makonni guda biyu a killace yana jinya biyo bahan kamuwar da yayi da ita wannan cuta tun a wasannin sada zumunta na ƙasa da ƙasa da Portugal ta fafata a wannan watan na Oktoba na shekarar 2020.
Ronaldo dai ya fasa buga wasanni da dama sakamakon wannan cuta daya kamu da ita inda bai samu camar fafata wasan da Portugal tayi da Sweden ba, haka baisami camar fafata gagarumin wasan da Juventus ta fafata da Barcelona ba a gasar zakarun nahiyar turai da Juventus tayi rashin nasara.
A baya dai anyiwa Christiano Ronaldo gwaji har sau biyu amma ana bayyana cewar bai warke ba inda sai a gwaji na uku wato a yammacin yau aka tabbatar ya warke daga cutar. Anasa ran Ronaldo zai dawo yin atisaye domin ci gaba da fafata wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Juventus.