A jiya Juma’a aka fara fafata wasannin share fage na mai girma gwamnan jahar Katsina wato Honourable Aminu Bello Masari. Inda aka fafata wasanni guda uku a jiyan wato da safe da rana da kuma yamma.
A wasannin da aka fafata a ranar farkon ta jiya Junior Katsina United ta lallasa Garkuwa FC daci 2 da nema. ‘Yan wasa Salihu Sani da Shamshu Ibrahim ne suka jefa ƙwallayen.
Ita kuwa Katsina United B ta rugurguza Dadinkowa daci 4 da nema ta hannun ‘yan Abubakar Abdullahi a mintina na 4 da Massaly Boubakar a daidai mintina na 45’l da 53. Sannan Nafiu Ibrahim ya sake saka tasa a daidai mintina na 84.
A wasa na uku kuwa Katsina United A tasha da kyar a hannun Niger Tornadoes daci 1 mai ban haushi.
Mustapha Muhammed ne dai ya sami nasara saka ƙwallo a raga bayan an dawo daga hutun rabin lokaci wato a dai-dai mintina na 52.
Za aci gaba da fafata wasa a yau wato rana ta biyu kenan.
Kano Pillars zata fafata da Dadinkowa.
Garkuwa F/C da Sokoto United.
Rarara da Danburan F/C.
Katsina United B da Zamfara United.