A wannan rana ta Litinin 2 ga watan Nuwamba za a shiga rana ta huɗu a gasar nan da ake fafatwa a jahar Katsina wato gasar share fage ta gwanna Aminu Bello Masari.
Wasannin dai dukkaninsu ana fafatasu a filin wasa na Muhammad Dikko dake birnin na Katsina. Inda wasannin suke batar da nishaɗi sosai da sosai ganin yadda aka fara dukan manyan ƙungiyoyi.
Ga jerin wasannin da za a fafata a yau Litinin:
Zamfara da Rarara Academy.
Sokoto United da Junior Katsina United
Garkuwa da Plateau United.
Katsina United A da Wikki Tourists.
Wasannin dai ana fafatasu a kowacce rana kuma ahaka za a ci gaba har a fita daga rukunin.